Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-25 16:32:31    
Kasar Sin na bunkasa wasannin motsa jiki ta hanyar yin amfani damar shirya taron wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008

cri

Kasar Sin ta samu nasarori da yawa a fannin wasannin motsa jiki a 'yan shekarun baya, musamman ma a taron wasannin motsa jiki na Olympics na Aden a shekarar 2004 ; Ban da wannan kuma za ta shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics a shekarar 2008 a nan Beijing.

Sashen kula da sha'anin wasannin motsa jiki na gwamnatin kasar Sin wato babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin, a kwanakin baya ba da dadewa ba, a nan Beijing, ta kaddamar da daftarin shirin bunkasa sha'anin wasannin motsa jiki nan da shekaru biyar masu zuwa. A cikin daftarin shirin, an jaddada, cewa za a yi amfani da damar shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008 wajen daga matsayin da gwamnatin kasar Sin take tsayewa a kai a fannin kara samar wa jama'ar kasar ayyukan hidimomi da kyau, wadanda suka shafi wasannin motsa jiki, kamar su samar musu wuraren motsa jiki da kayayyakin motsa jiki da dai sauran makamantansu. A sa'i daya kuma, za a yi amfani da zarafin shiryawa da kuma shiga cikin taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing wajen daga matsayin kasar Sin a fannin wasannin motsa jiki daga dukkan fannoni.

A gun wani taron watsa labaru da aka shirya a nan Beijing, shugaban babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin Mr. Liu Peng ya furta, cewa: babbar manufar bunkasa wasannin motsa jiki da za a aiwatar da ita nan da shekaru biyar masu zuwa, ita ce mayar da shiryawa da kuma shiga wasannin motsa jiki na Olympics na shekarar 2008 a matsayin wata kyakkyawar damar gudanar da ayyukan wasannin motsa jiki na dukan jama'ar kasar, da kafa tsarin ayyukan wasannin motsa jiki na jama'a dake da sigar musamman bisa mataki na farko domin share hawayen jama'a har ba fashi, wadanda suke kishin yin wasannin motsa jiki da samun ilmi, ta yadda za a kyautata lafiyar jikin 'yan kabilun kasar, da daga matsayin wasannin motsa jiki da kuma kara karfin da kasar Sin take da shi na yin karawa a fannin wasannin motsa jiki. Mr. Liu Peng ya jaddada, cewa dole ne 'yan wasan kasar Sin su yi namijin kokari wajen samun horaswa domin samun kyakkyawan sakamako a gun taron wasannin motsa jiki na Olympics na shekarar 2008 da kuma sauran gagaruman gasannin da za a gudanar tsakanin kasa da kasa, ta yadda za su nemi daukaka kwarjinin kasa mahaifa, da zurfafa gyare-gyaren tsarin wasannin motsa jiki har ba fashi da kuma sanya kokari matuka wajen yalwata sana'ar wasannin motsa jiki.

Sa'annan Mr. Liu Peng ya yi farin ciki matuka da fadin, cewa ko shakka babu taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing zai samar da kyakkyawar dama da ba za a iya kimantawa ba ga yunkurin yalwata sha'anin wasannin motsa jiki na kasar Sin. Ya kara da, cewa nan da shekaru biyar masu zuwa, wajibi ne a yadada amfanin da taron wasannin motsa jiki na Olympics ke bayarwa yayin da ake bunkasa sha'anin wasannin motsa jiki na kasar Sin.

Game da wasannin motsa jiki na jama'a, Mr. Liu Peng ya fadi, cewa Shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics da za a yi zai kara sa kaimi ga jama'ar kasar wajen shiga wasannin motsa jiki, da kuma ilmantar da kowa a fannin wasannin motsa jiki har ya zama tamkar irin karfin ingizawa na gina lafiyar jikin jama'ar kasar. Mr. Liu Peng ya ci gaba da, cewa a fannin wasannin karawa, yawan ire-iren wasanni da kuma yawan 'yan wasanmu za su shiga dukkansu za su kafa sabon tarihi. Babu tantama, ta wannan taron wasannin Olympics, za mu horar da wassu kwararru masu kula da harkokin wasannin karawa da kuma alkalai.

Kazalika, Mr. Liu Peng ya fadi, cewa gudanar da taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing zai samar da zarafi ga da'irorin wasannin motsa jiki na kasar Sin wajen koyon salon zamani da kwamitin wasannin motsa jiki na Olympics na kasa da kasa da kuma sauran kungiyoyin wasannin motsa jiki suke bi don tafiyar da harkokin wasannin motsa jiki a fannin kasuwanci. Hakan zai amfana wa kasar Sin wajen daga matsayin kasar Sin a fannin raya dukiyoyin wasannin motsa jiki da kuma daukaka ci gaban sana'ar wasannin motsa jiki na kasar Sin.

A cikin daftarin shirin, an tabbatar da manufofin yalwatuwa nan da shekaru biyar masu zuwa a fannin wasannin motsa jiki na jama'a, da wasannin karawa da kuma na sana'ar wasannin motsa jiki da dai sauran fannoni. Mr. Liu Peng ya bayyana, cewa abu mafi muhimmanci dake cikin manufofin shi ne wasannin motsa jiki na jama'a. Dalili kuwa, shi ne gwamnatin kasar Sin tana dukufa kan aikin bunkasa wasannin motsa jiki ne domin samar da kyakkyawar hidima ga jama'ar kasar wajen yin wasannin motsa jiki, da daga matsayin lafiyar jikinsu. (Sani Wang )