|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2006-08-25 16:32:07
|
Ingancin ruwa na sashen kogin Songhuajiang da ke lardin Jilin na kasar Sin ya kai ma'aunin da aka tanada domin kiyaye muhali
cri
Bayan aukuwar matsalar kazancewar ruwa cikin wani reshen kogin Songhuajiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin, kuma bayan da gwamnatin wurin ta yi aiki tukuru, sai a hana yaduwar kazancewar ruwa cikin nasara. Sakamakon binciken da sassan kiyaye muhalli suka yi a wannan sashen kogin ya bayyana cewa, Ingancin ruwa na sashen kogin Songhuajiang da ke lardin Jilin na kasar Sin ya kai ma'aunin da aka tanada domin kiyaye muhali sosai.
Wani bayanin da gwamnatin lardin Jilin na kasar Sin ta gabatar a ran 24 ga wata ya bayyana cewa, ba a samu mutane ko dabbobi da suka sha dafi a bakin kogin ba. Yanzu ruwan da aka kazamta ya riga ya shiga cikin kogin Songhuajiang, kuma ba a samu abubuwan kazantarwa daga cikin wannan kogi ba. (Umaru)
|
|
|