Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-25 16:29:03    
Kauye mai suna "Jinshan" a kudancin birnin Shanghai na kasar Sin

cri

Kauye mai suna "Jinshan" yana kudancin birnin Shanghai, birnin masana'antu da kasuwanci mafi girma a kasar Sin. Abin da ake nufi da "Jinshan" cikin Sinanci shi ne wuri mai arziki. Amma a cikin wani tsawon lokaci da ya wuce, matsayin bunkasuwar tattalin arzikin wannan kauye yana baya-baya ainun, idan an kwatanta shi da na sauran yankuna na birnin Shanghai. Sannu a hankali yanzu, kauyen ya sami sauye-sauye a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce.

Tun can zamanin da, aikin noma shi ne babbar sana'a ga mutanen kauyen "Jinshan". Kudin shiga da suke samu kadan ne. Manomi mai suna Song Jie da ke zama a wannan kauye shi ma haka yake a da. Ya gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa, a da ya kan yi kokari sosai wajen neman kudi don ciyar da iyalinsa, amma yanzu kudin shiga da yake samu ya ishe shi a 'yan shekarun nan da suka wuce. Ya kara da cewa, "a da, yawancin gidajen kwana na manoman kauyenmu benaye ne masu hawa daya kawai, amma yanzu yawancinsu sun riga sun gina kyawawan gidajensu na banaye masu hawa da dama. Ban da wannan kuma an shimfida hanyoyin mota da ke zuwa bakin duk gidajen manoman kauyenmu. Dadin dadawa an gina dakin shakatawa na tsoffafi, da dakin shan magani, da wurin wasannin motsa jiki da makamantansu a kauyenmu, yanzu muna more su yadda muka ga dama. "

Kauyen "Jinshan" ya sami ci gaba kamar haka ne a cikin shekaru uku kawai. Yanzu an riga an raya kauyen nan mai fadin muraba'in kilomita sama da 580 da ya zama wani wuri kamar wani karamin birni yake. Malam Liu Zhengxian, jami'in hukumar kauyen da abin ya shafa ya bayyana cewa, "jimlar kudi da kauyen "Jinshan" ya samu daga aikin masana'antu ya wuce kudin Sin Yuan biliyan 61 a shekarar bara. Matsakaicin jimlar kudin da kauyen ya samu a ko wace shekara ta kan karu da kashi 33.8 cikin dari har cikin shekarun nan biyar da suka wuce. Yanzu an riga an kafa tsarin masana'antu a kauyen wanda ya fi dogara da masana'antun sarrafa magunguna da magungunan sha, da na'urori masu aiki da wutar lantarki, da kayayyakin gyaran motoci da kuma masakar tufafi. "

Abin da ya fi jawo hankulan mutane shi ne, a lokacin da ake samun ci gaba da sauri wajen bunkasa aikin masana'antu a kauyen "Jinshan", ba a gurbata muhallinsa ba. Malam Liu Zhengxian, jami'in hukumar kauyen ya kara da cewa, kullum hukumar kauyansa tana kokari sosai wajen hana a gurbata muhalli, don neman samu ci gaba mai dorewa wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da na zamantakewar al'umma. Ya ce, "kauyenmu ya gudanar da shirin kare muhalli na shekaru uku wato a tsakanin shekarar 2003 zuwa ta 2005. A karkashin shirin nan, mun kafa tashar binciken yanayin iska mai aiki da kanta, masana'antu 39 sun yi amfani da makamashi da ba ya gurbata muhalli maimakon kwal, mun dasa bishiyoyi a filaye masu fadin kadada sama da 1000, mun kyautata rafuka da yawansu ya kai 7. Ta haka mun kare muhalli da kyau,"

Ka zalika kauyen nan ya yi kokari sosai wajen bunkasa harkokin yawon shakatawa. Bisa kidayar da aka yi, an ce, yawan kudi da kauyen ya samu daga wajen harkokin yawon shakatawa ya kai kudin Sin Yuan miliyan 250 a shekarar bara. Yawan mutane da suka yi yawon shakatawa a kauyen shi ma ya kai dubu 450 a bara.

Yanzu, mutanen kauyen "Jinshan" sun hakake cewa, tabbas ne, za su cim ma manufarsu wato za su raya kauyensu da ya zama wani wuri mafi kyau a birnin Shanghai kuma a duk kasa baki daya. (Halilu)