Kwanakin baya ba da dadewa ba, wani jami'in gurin ibada na Yasukuni ya furta, cewa kalmomin bayyana dalilin tayar da yakin kai hari da kasar Japan ta yi wadanda aka fada a dakin Yushukan mallakar gurin ibada na Yasukuni suna da kurakurai. Don haka, an bayyana ra'ayin kuskure game da tarihi ga jama'ar Japan don su kauce wa hanyar gaskiya.
Bangaren gurin ibada na Yasukuni ya yi nuni da, cewa an fadi kalmomin bayani cewar wai kasar Japan ta bayar da yakin kai hari ga kasar Sin da kuma kai harin ba zata kan tashar ruwa ta Pearl Harbor ne domin kasar Amurka ta garkama wa kasar Japan takunkumin tattalin arziki. Lallai an bayyana ra'ayin kuskure a fannin tarihi ga jama'a' Japan don su kauce wa hanyar gaskiya. Saboda haka ne, gurin ibada na Yasukuni ya tsaida kudurin sake rubuta kalmomin bayani. Amma, bangaren da abun ya shafa bai fayyace abubuwan dake cikin kalmomin ba. ( Sani Wang )
|