A gun cikakken zama na 26 na hadaddiyar kungiyar kasa da kasa a fannin ilmin taurari da aka gudanar da shi a ran 24 ga watan nan a birnin Prague na kasar Szech, inda aka jefa kuri'a don tabbatar da ma'anar sabbin taurari na sararin samaniya. Bisa sabuwar ma'anar sabbin taurari da aka bayyana, an ce, tsarin rana na da manyan taurari guda 8, wato ke nan aka fitar da tauraron Pluto daga jerin ' Manyan Taurari 9' na tsarin rana, wanda kuma aka saukar da matsayinsa zuwa na ' tauraron Dwarf Planets' .
Masana ilmin taurari da yawansu ya kai 2,500 daga kasashe da jihohi 75 na duk duniya sun shiga jefa kuri'ar.
Har kullum akan yi gardama kan tauraron Pluto tun bayan da aka gano shi a shekarar 1930 saboda girmansa da kuma nauyinsa na hakika kadan ne idan an kwatanta su da na sauran taurarin sararin samaniya.
Sabuwar ma'ana ta bayyana, cewa manyan taurari guda 8 ne dake kewayan rana, wato su ne tauraron Mercury, da tauraron Venus, da tauraron duniya, da tauraron Mars, da tauraron Jupiter, da tauraron Saturn, da tauraron Uranus da kuma tauraron Neptune.
An kawo karshen taron ne a wannan rana. Shugaban hadaddiyar kungiyar kasa da kasa a fannin ilmin taurari Mr. Ronald D. Ekers ya shelanta, cewa kasar Sin ta samu iznin shirya babban taro na 28 na kungiyar din a shekarar 2012. ( Sani Wang )
|