Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-25 15:04:54    
Hanyar yin shawarwari wata hanya ce da ta fi kyau wajen warware matsalar nukiliya ta Iran

cri

Ran 22 ga wata, bayan da kasar Iran ta ba da amsa kan shirin kuduri na kasashe 6, wato kasashen Amurka, da Rasha, da Sin, da Ingila, da Faransa, da kuma Jamus, kasashen Rasha da Sin sun yi bayani daya bayan daya cewa, suna fatan ci gaba da warware matsalar nukiliya ta Iran cikin lumana ta hanyar diflomasiya da yin shawarwari, bisa tushen tsarin hana barbazuwar nukiliya na duniya. Wannan ne kuma fata na yawancin kasashen duniya da ra'ayin jama'a.

Kasar Iran ta soma ayyukan ayautar makamashin nukiliya a shekaru 50 na karni 20, a lokacin ta samun goyon baya daga kasar Amurka, da kuma sauran kasashen yamma. Bayan da kasashen Amurka da Iran suka dakatar da huldar jakadanci a shekarar 1980, sau da yawa kasar Amurka ta zargi kasar Iran, sabo da ta bunkasa makaman nukiliya a siri ta hanyar wai "yi amfani da makamashin nukiliya cikin lumana", kuma ta dauki "manufar yin tarnaki " ga kasar Iran. A hakika dai, matsalar nukiliya ta Iran ta nuna dangantakar da ke nukura da juna a tsakanin kasar Iran da wasu kasashe, inda suka hada da kasar Amurka.


Matsalar nukiliya ta Iran wata matsala ce mai yamutsi sosai. Ta ayyukan bincike da aka yi wa kasar Iran har shekaru 3, hukumar makamashin nukiliya ta duniya ba ta gano kasar Iran ta yi amfani da kayayyakin nukiliya da ta gabatar da rokon rajista kan makaman nukiliya ba. Sabo da haka, hukumar ba ta iya shaida cewa, kasar Iran tana da kayayyakin nukiliya da ba ta gabatar da rokon rajista ba, ko tana aiwatar da ayyukan nukiliya a boye.

Sabo da haka, bai kamata a kai hari kan kasar Iran ba, wannan ba zai iya warware matsalar nukiliya ta Iran ba; hanyar yin takunkumi wajen tattalin arziki kuma ba ta iya warware wannan matsla ba. Idan kasar Amurka ta kara tayar da wani yaki, watakila ba ta da isasshen karfi wajen yaki, kuma za a kara tabarbarewar halin da shiyyar gabas ta tsakiya ke ciki.

Manazarta suna ganin cewa, idan gwamnatin jam'iyyar kwaminis ta kasar Amurka tana fatan samun nasara a zaben da za a yi a tsakiyar watan Nuwamba na shekarar da muke ciki, tilas ne ta samun sakamako mai kyau kan matsalar nukiliya ta Iran. Watakila wannan ne dalili daya da kasar Amurka tana neman kara saurin gudanarwar yin takunkumi wajen tattalin arziki ga Iran.
Amma, kasar Iran kasa ce ta fi girma ta 4 na duniya wajen fita da man fetur, ita ce kuma kasa ta biyu wajen fitar da man fetur a cikin kungiyar OPEC. Yi wa takunkumi ga kasar Iran zai kara yawan farashin man futur na duniya, haka kuma za a murkushe tattalin arziki na kasashen yamma.



Abin da ya fi damuwa shi ne, idan kasar Iran ta yi kangiya a mashigin tekun Hormuz, wato ta yanka muhimmiyar hanyar jigilar da man fetur kashi 20 cikin dari bisa na duk duniya, wannan zai kawo tasiri mai tsanani sosai ga bunkasuwar tatalin arziki ta duniya.

A 'yan shekarun da suka wuce, hali mai tsanani da matsalar nukiliya ke kawowa kasar Iran ya riga ya sanya masu zuba jari na kasashen waje su janye jiki daga kasar, haka kuma matsalar rashin kudi ta hana bunkasuwar tattalin arziki ta Iran.

A takaice dai, ko kai hari, ko yin takunkumi na tattalin arziki, dukansu ba kawai ba su da taimako kan warware matsalar nukiliya ta Iran ba, har ma za su kara yawan yamutsi da lahanta moriya na bangarori daban daban. Idan bangarori daban daban da ke da nasaba su tsaya kan yin tattaunawa, da warware matsalar nukiliya ta Iran ta hanyar lumana, wannan zai yi amfani ga zaman lafiya, da zaman karko, da kuma bunkasuwar shiyoyyi da duk duniya.