Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar a ran 25 ga wata an ce, a wannan shekarar da muke ciki tsarin yin ceto na zirga-zirgar kasar Sin ya riga ya ceci mutane kusan 500 da suka gamu wa da hadarurruka.
Bisa sabuwar kididdigar da ma'aikatar zirga-zirga ta kasar Sin ta yi an ce, zuwa farkon watan Agusta na wannan shekara, yawan ayyukan musamman da tsarin yin ceto na zirga-zirgar kasar Sin ya yi ya kai 49, wato an ceci jiragen ruwa 32 cikin nasara.
Tun farkon wannan shekara zuwa yanzu, an yi ta yin guguwai a shiyyoyin bakin tekun da ke kudu maso gabashin kasar Sin, tsarin yin ceto na zirga-zirgar kasar Sin ya ba da babban taimako ga ayyukan yin ceton mutane masu shan bala'i da tsamo mutane daga cikin ruwan teku.
A wata sabuwa kuma an ce, zuwa shekarar 2010, kasar Sin za ta kafa cikakken tsarin yin ceto a shiyyoyin tekuna 3 wato tekun Beihai da tekun gabas da tekun kudu daga cikin teku da kuma sararin sama. (Umaru)
|