A ran 24 ga wata a birnin Abuja, hedkwatar kasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo, shugaban kasar ya sanar da cewa, manufar gyare-gyaren kurkuku da gwamnatin Nijeriya ke tafiyar da ita ta riga ta sa fursunoni wajen dubu 10 sun sake samun 'yanci.
Mr. Obasanjo ya ba da wannan labari ne yayin da yake yin bayani kan manufar da gwamnatin kasar ta dauka game da yin gyare-gyaren kurkuku. Sa'an nan kuma ya yi kira da a kafa wani asusu don tattara kudi domin kyautata sharudan kurkuku.
Sabo da ci gaban da aka samu wajen gudanar da ajandun shari'a ba shi da sauri, kuma tsarin tafiyar da harkokin kurkuku ya yamutsa, shi ya sa har yanzu da akwai fursunonin da yawansu ya wuce kashi 50 bisa 100 da ke cikin kurkukun Nijeriya wadanda ba a yanke musu hukunci ba tukuna. Bisa shirin gyare-gyaren kurkukun da kwamitin FEC wato kwamitin zartarwa na Tarayyar ya kaddamar da shi a farkon wannan shekara, an ce, yawan fursunonin da za a sake su daga kurkukun Nijeriya ya kai dubu 250. (Umaru)
|