Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-24 20:29:39    
Mutane 4 sun mutu a sakamakon cutar kwalara a kasar Kodivwa

cri

Ma'aikatar kiwon lafiyar jama ta kasar Kodivwa ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu, mutane 4 sun riga sun mutu a sakamakon cutar kwalara a birnin Abidjan, babban birnin tattalin arziki na kasar Kodivwa, haka kuma wasu mutane 41 sun kamu da cutar.

Bisa labarin da muka samu, an ce, da farko an gano cutar kwalara ne a wani yankin matalauta na tashar jirgin ruwa na Bouet da ke Abidjan a farkon watan Yuli, sa'an nan cutar ta fara yaduwa a sauran wurare. Ma'aikatar kiwon lafiyar jama ta riga ta dauki matakai cikin gaggawa domin shawo kan cutar da ba kwantar da majiyyata a asibitoci ba tare da biyan kudi ba, haka kuma ta yi gargadi a kan jama'a da su kula da lafiyar abinci da ruwan sha.(Danladi)