Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-24 18:22:26    
Sabuwar dokar Sin za ta ba da kariya ga dukiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu

cri
A wannan mako, majalisar dokoki ta kasar Sin tana dudduba shirin doka dangane da ikon mallakar dukiyoyi a karo na biyar wanda aka taba yin gardama sosai a kai a kasar.

Dokar nan wata doka ce mai tushe dangane da amincewa da dukiyoyi da yin amfani da su da kuma kare su, haka kuma dokar ita ce wata doka mai muhimmanci don daidaita ikon mallakar dukiyoyi. Yau da shekaru biyu da suka wuce, an rubuta wata sabuwar ka'ida kada a taba halaltattun dukiyoyin jama'a masu zaman kansu a cikin gyararren shirin tsarin mulki na kasar Sin. Bayan haka majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato majalisar dokoki ta kasar ta sha yin bincike a kan shirin doka kan ikon mallakar dukiyoyi. A lokacin da majalisar ke dudduba wannan shirin doka, wata matsalar ka'ida da aka yi gardama mai zafi a kai ita ce, yaya za a kare dukiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu, a kasar Sin wadda tsarin mallakar gwamnati ya zama ginshikin tsarin tattalin arziki?

A cikin shirin dokar da aka gabatar wa majalisar don dudduba ta a wannan gami, an bayyana a fili cewa, wajibi ne, a kare tsarin muhimmin tattalin arzikin kasar, kuma wajibi ne, a kare dukiyoyin gwamnati da kungiyoyi da na jama'a masu zaman kansu cikin daidaici.

Yayin da Malam Hu Kangsheng, mataimakin shugaban kwamitin shari'a na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ke yin bayani a kan wannan shirin doka, ya bayyana cewa, "wajibi ne, a tsaya tsayin daka wajen gudanar da tsari mai tushe na tattalin arzikin kasar Sin da kare dukiyoyin gwamnati da na kungiyoyi da jama'a masu zaman kansu cikin daidaici. In ba a gudanar da wannan tsari mai tushe ba, to, za a canja ainihin tsarin mulkin gurguzu. Haka kuma in ba a kare dukiyoyin cikin daidaici ba, to, za a saba wa ka'idojin tattalin arziki na kasuwanni. Akasin haka za a lahanta tsari mai tushe na tattalin arziki. "

A cikin wannan shirin dokar, an bayyana cewa, za a inganta kare dukiyoyin gwamnati, don hana a mayar da su cikin hannayen mutane. Duk wanda ya mayar da dukiyoyin gwamnati cikin hannayen mutane, ko shakka babu, za a yanke masa hukunci bisa shari'a. Malam Hu Kangsheng ya yi bayani a kan wannan cewa, "a zahirin gaskiya, yanzu ana taba dukiyoyin gwamnati sosai a fannin tattalin arziki. Sabo da haka, a cikin doka kan ikon mallakar dukiyoyi, wajibi ne, an rubuta ka'idoji game da inganta kare dukiyoyin gwamnati, don kada a mayar da su cikin hannayen mutane masu zaman kansu. "

A sakamakon karuwar dukiyoyin 'yan birane na kasar Sin da sauri, 'yan biranen suna mai da hankali sosai ga doka kan ikon mallakar dukiyoyi. A kayukan kasar kuma, filaye sun zama manyan dukiyoyi ga manoma. Wannan shirin dokar ba ta kara samar da damar musayar filayen da saye da sayar da su ba. Malam Hu Kangsheng ya ce, dalilin da ya sa haka shi ne domin kare moriyar manoma da gonakinsu. Ya kara da cewa, wajibi ne, a gudanar da tsarin kare gonaki a tsanake a kasar Sin, domin filaye sun yi kadan, mutane kuma sun yi yawa a kasar. Yanzu, ba a kafa tsarin ba da tabbacin zaman rayuwa ga duk manoma na kasar Sin ba, ikon mallakar gonaki ta hanyar kwangila da ikon amfani da filaye suna ba da tabbaci ga manoma wajen yin aikin noma da zaman rayuwa. Bisa halin da ake ciki yanzu a kasar Sin, ba zai yiwu a kara samar da ikon saye da sayar da gonaki ko filaye yadda aka ga dama ba." (Halilu)