Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-24 15:27:47    
Kawancen demokuradiyya da 'yanci na Taiwan

cri

Takaitaccen sunan kawancen demokuradiyya da 'yanci na Taiwan shi ne "kawancen Taiwan", kuma wani kawancen siyasa ne wanda yake hade da mutanen lardin Taiwan da ma'aikatan gurguzu da masu kishin kasa wadanda ke nuna goyon bayansu ga zaman gurguzu, kuma wata jam'iyyar siyasa ce wadda take yin hidima ga zaman gurguzu, wadda kuma ta shiga cikin harkokin kasa ta hanyar hadin gwiwa a tsakaninta da J.K.S.

Bayan da aka kafa kawancen Taiwan a ran 12 ga watan Nuwamba na shekarar 1947 a Hongkong, sai ta dukufa kan sabon juyin-juya halin demokuradiyya, a watan Mayu na shekarar 1948, ta bayar da "sanarwa ga 'yanuwanmu na Taiwan", kuma ta aike da wakilinta don halartar taro na farko na dukkan wakilan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta farko ta jama'ar Sin da yin zaben gwamnatin tsakiya ta jama'a, kuma ta ba da taimako ga kafa sabuwar kasar Sin.

Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, daga wani fanni kawancen Taiwan ya yi kokarin shiga zaman rayuwar siyasa na kasa da yin harkokin Taiwan da kyau, daga wani fanni daban kuma mambobin kawancen sun nuna kwarewarsu a gurabun ayyukansu, kuma sun yi matukar kokari domin wadatar da kasar mahaifa. Bayan da aka shiga cikin sabon lokacin tarihi a shekarar 1978, kawancen Taiwa ya juya hankalinsa kan muhimmin aikin raya zaman gurguzu na zamani. Bisa matsayin wata jam'iyyar siyasa da ta shiga cikin harkokin kasa, kawancen Taiwan ya ba da shawarwarinsa kan harkokin kasa, kuma ya ba da babban taimako ga sha'anin raya zaman gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin da sa kaimi ga yunkurin tarihin da ake yi domin samun dinkuwar kasar mahaifa daya cikin lumana.

Yawancin mambobin kawancen Taiwan su ne mutanen da suke aiki a sassan ba da ilmi da kimiyya da fasaha da aikin likitanci da tattalin arziki da wasannin fasaha da watsa labaru da madaba'u. Kawancen yana da babban zumunci kuma yana yin mu'amala sosai a tsakaninsa da 'yanuwanmu na Taiwan da ke tsibirin Taiwan da kasashen waje. Shugabar kawancen Taiwan na yanzu ita ce Lin Wenyi.(Umaru)