Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-24 15:23:25    
Iran tana fatan sassa daban-daban za su koma kan teburin shawarwari

cri
A ran 23 ga wata, Hamid Reza Asefi, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Iran ya bayyana cewa, amsar da Iran ta bayar ga tsarin kasashe 6 mai yakini ne, kuna tana fatan sassa daban-daban da abin ya shafa za su koma teburin shawarwari tun da wuri. A wannan ranar kuma majalisar harkokin kasashen waje ta Amurka ta bayyana cewa, amsar da Iran ta bayar ba ta biya bukatar da kuduri mai lamba 1696 na kwamitin sulhu na M.D.D. ya gabatar ba, inda ya nemi Iran da ta dakatar da shirinta na tace sinadarin Uranium.

Mr. Asefi ya bayyana cewa, Iran ta bayar da cikakkiyar amsa kan tsarin da kasashen 6 suka gabatar kuma daga duk fannoni, inda a ciki Iran ta gabatar da shawarwari da tambayoyinta game da yadda za a sake yin hadin gwiwa da yin shawarwari tsakanin ta da kasashen 6.

A wannan rana kuma majalisar harkokin kasashen waje ta Amurka ta bayar da wata sanarwa cewa, amsar da Iran ta bayar ba ta biya bukatar da kudurin da abin ya shafa da kwamitin sulhu ya gabatar ba. Amurka tana nan tana yin nazari domin daukar matakan da za ta aikata a nan gaba. (Umaru)