Bisa labarin da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhau ya samu daga bangaren da abin ya shafa a kwanan baya, an ce, kasar Sin tana kokari sosai wajen yin ma'amala da hadin kai a tsakaninta da kasashe daban daban, yayin da take yaki da talauci. Tana yin amfani da gudummowa da take samu daga kasashen waje wajen daidaita batun yaki da talauci, kuma yanzu ta riga ta samu sakamako mai kyau.
An ruwaito cewa, ya zuwa yanzu, bankin duniya da kasar Sin sun riga sun yi ayyukan tallafa wa matalauta guda uku bisa rancen kudi da bankin ya bayar, yawan kudin gudummowa da bankin ya bayar ya kai dalar Amurka miliyan 610. Bayan da aka kammala ayyukan nan, yawan matalauta wadanda za su sami isasshen abinci da sutura zai wuce miliyan 8. Haka kuma wasu kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da kungiyoyi da ba na gwamnati ba su ma sun yi hadin kai da kasar Sin wajen yaki da talauci a fannoni daban daban, su ma sun sami sakamako mai kyau. (Halilu)
|