A ran 23 ga wata, an bude taron magungunan gargajiya na duniya a karo na 9 a birnin Nanning da ke kudu maso yammacin kasar Sin, masu aikin magungunan gargajiya fiye da 400 da suka zo daga kasashe 29 sun halarci taron.
Bisa labarin da muka samu, an ce, za a shafe kwanaki 3 ana yin taron, a gun taron, za a tattauna a kan kare magungunan gargajiya da yin amfani da su da kara sarrafa magungunan gargajiya da yin nazari a kan magungunan gargajiya ta fasahohin zamani da kare ikon mallakar ilmi dangane da haka da dai sauransu.(Danladi)
|