Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-23 20:27:50    
Kasar Sin da ke kan hanyar samun dinkuwar kasa

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malama Umm Salamah Ibrahim da ke zaune a birnin Zaria na jihar Kaduna da ke kasar Nijeriya. A cikin wasikar da ta aiko mana, ta tambaye mu, shin kasar Sin tana da cikakken ikon mulkin Hongkong? Kuma mene ne manufofin gwamnatin kasar Sin dangane da Taiwan?

Hongkong yankin kasar Sin ne tun lokacin da. Tun bayan da kasar Birtaniya ta tayar da yakin tabar Wiwi a shekara ta 1840, bi da bi ne ta tilasta wa gwamnatin daular Qing da ta sa hannu a kan jerin yarjejeniyoyi marasa adalci, kuma ta wadannan yarjejeniyoyi ne, ta yanke tsibirin Hongkong da kuma kuriyar zirin Jiulong daga kasar Sin har illahmasha-Allah, kuma ta tilasta wa kasar Sin da ta ba da hayar makeken yanki da ke arewacin zirin Jiulong da kuma tsibirai sama da 200 da ke dab da zirin.

Bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, matsayin da gwamnatin kasar Sin ta dauka a kullum shi ne, Hongkong wani yanki ne na kasar Sin, kuma kasar Sin ba ta amince da yarjejeniyoyi marasa adalci da kasashe masu mulkin danniya suka tilasta mata. Tun daga shekara ta 1982, gwamnatocin kasashen Sin da Birtaniya sun yi shawarwari a jere dangane da batun Hongkong, kuma daga karshe, a ran 19 ga watan Disamba na shekara ta 1984 a hukunce ne, bangarorin biyu suka rattaba hannu a kan sanarwar hadin gwiwa dangane da batun Hongkong a nan birnin Beijing, inda suka sanar da cewa, gwamnatin Birtaniya za ta mayar da Hongkong a karkashin jagorancin jamhuriyar jama'ar kasar Sin a ranar 1 ga watan Yuli na shekara ta 1997, a sa'i daya kuma, gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin za ta maido da ikon mulkin Hongkong daga ran 1 ga watan Yuli na shekara ta 1997.

A ran 1 ga watan Yuli na shekara ta 1997, da misalin karfe 12 na dare, an daga tutar jamhuriyar jama'ar kasar Sin da ta yankin musamman na Hongkong a Hongkong, Hongkong ta koma gida ke nan. Gwamnatin kasar Sin tana da cikakken ikon mulkin Hongkong, amma a sa'i daya kuma, bisa ka'idar 'kasa daya amma tsarin mulki biyu', ana gudanar da tsarin musamman a Hongkong, kuma Hongkong tana da ikon tafiyar da harkokin kanta. Ba a gudanar da tsari da manufofi na gurguzu a Hongkong ba, kuma Hongkong tana iya ci gaba da gudanar da tsarinta na jarin hujja. Hongkong yana karkashin jagorancin gwamnatin tsakiya kai tsaye, amma kuma, yana da ikon tafiyar da harkokin kansa, ban da harkokin diplomasiyya da na tsaron kasa wadanda gwamnatin tsakiya ce ke kula da su, Hongkong yana da ikon gudanar da harkokin kanta da ikon kafa doka da ikon cin gashin kai a fannin shari'a da kuma ikon koli na shari'a, kuma mutanen Hongkong ne suke tafiyar da harkokin kansu.

Yanzu bari mu juya mu ga batun Taiwan. A ran 1 ga watan Oktoba na shekara ta 1949, jamhuriyar jama'ar kasar Sin ta kafu. Amma a sa'i daya, kusoshin jam'iyyar Kuomintang sun janye jikinsu har zuwa lardin Taiwan na kasar Sin, bisa goyon bayan rukunonin waje, sun yi adawa da gwamnatin tsakiyar kasar Sin, daga nan batun Taiwan ya fito.

Daidaita batun Taiwan da tabbatar da samun dinkuwar kasar Sin babbar moriyar al'ummar kasar Sin ce. A cikin shekaru 50 da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta yi ta kokartawa ba tare da kasala ba don neman cimma wannan buri. Ka'idar Sin daya tak a duniya babban tushe ne na manufofin gwamnatin kasar Sin a kan Taiwan. Gwamnatin kasar Sin da jama'arta suna nacewa ga bin ka'idar Sin daya tak a duniya, wato akwai kasar Sin guda daya tak a duniya, Taiwan wani kashi ne na kasar Sin, ba wanda ya iya rarraba mulkin kan kasar Sin da kuma yankin kasar. Gwamnatin kasar Sin da jama'arta suna tsayawa tsayin daka kan yin adawa da duk wani makirci na neman jawo baraka ga kasa da kuma al'umma, haka kuma suna tsayawa kan yaki da ko wane yunkuri na neman kirkiro 'Sin biyu', ko 'Sin daya Taiwan daya' ko kuma 'neman 'yancin kan Taiwan'.

Ban da wannan, a gun taro na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta goma wanda aka yi a ran 14 ga watan Maris na shekara ta 2005, an kuma zartas da 'dokar hana jawo baraka ga kasa'. Dokar ta nuna cewa, akwai kasar Sin guda daya kawai a duniya, babban yankin kasar Sin da kuma Taiwan dukansu yankuna ne na kasar Sin, ba wanda ya iya rarraba mulkin kan kasar Sin da kuma yankunanta. Kiyaye mulkin kan kasa da kuma cikakken yankinta nauyi ne da ke bisa wuyan dukan jama'ar kasar Sin, ciki har da jama'ar Taiwan. Kasar Sin ba za ta yarda da 'yan a-ware na Taiwan da su cire Taiwan daga kasar Sin bisa ko wane dalili da kuma ta ko wace hanya ba. Batun Taiwan ya fito ne sakamakon yakin basasa na kasar Sin. Daidaita batun Taiwan da tabbatar da dinkuwar kasar Sin harkar gida ce ta kasar Sin, wadda bai kamata rukunonin kasashen waje su tsoma baki a ciki ba. Tsayawa kan ka'idar Sin daya tak a duniya tushe ne a wajen tabbatar da dinkuwar kasar Sin cikin lumana. Tabbatar da dinkuwar kasar Sin ta hanyar lumana ya dace da babbar moriyar jama'ar gabobi biyu na zirin Taiwan. Da sahihin zuci ne kasar Sin za ta yi iyakacin kokarinta a wajen tabbatar da dinkuwar kasa cikin lumana. Bayan da aka samu dinkuwar kasa cikin lumana kuma, Taiwan za ta iya gudanar da wani tsarin mulki da ya sha bamban da na babban yankin kasar Sin, kuma tana da cikakken ikon tafiyar da harkokin kanta.

Bayan da gwamnatin kasar Sin ta maido da ikon mulki a Hongkong da Macao bi da bi, dukan jama'ar kasar Sin suna matukar son ganin cewa, za a daidaita batun Taiwan tun da wuri, don cimma burin samun cikakkiyar dinkuwar kasa. Muna imani da cewa, bisa kokarin da dukan jama'ar kasar Sin, ciki har da jama'ar gabobi biyu na zirin Taiwan da kuma Sinawa mazauna kasashen waje, suke yi tare, tabbas ne za a iya tabbatar da samun dinkuwar kasar Sin. (Lubabatu)