A ran 22 ga wata, kasar Iran ta ba da amsa a rubuce kan shirin kuduri na kasashe 6, a ran 23 ga wata, kasashen duniya sun mai da martani kan wannan.
A ranar 23 ga wata, ofishin kakakin Ma'ikatar harkokin waje ta kasar Sin ya ba da amsa ga manema labaru, inda ya bayyana cewa, bangaren Kasar Sin yana ganin cewa, warware matsalar nukiliyar Kasar Iran cikin lumana ta hanyar yin shawarwarin diflomasiya shi ne zabi mafi kyau, kuma ya dace da moriyar bangarori daban daban. Bangaren Sin yana fatan bangaren Iran ya dauki wajaban matakai masu yakini, kuma yana fatan sauran bangarori daban daban za su yi hakuri don samar da dama mai kyau don farfado da shawarwarin zaman lafiya.
A ran nan, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Rasha ta bayar da wata sanarwa inda aka bayyana cewa, kasar Rasha za ta ci gaba da yin kokari domin warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar siyasa, kuma hukumar makamashin nukiliya ta duniya ta bayar da gudummowa mai muhimmanci a kan haka.
A ran 23 ga wata, minstan harkokin waje na kasar Faransa Philippe Douste-Blazy ya bayyana a birnin Paris cewa, kasar Faransa tana son yin shawarwari tare da kasar Iran, amma sharadi shi ne kasar Iran ta daina tace sinadarin Uraninum.
A ran 22 ga wata, John R. Bolton, wakilin din din din na kasar Amurka da ke M.D.D. ya bayyana cewa, kasar Amurka za ta yi nazari kan amsar da Iran ta bayar, idan amsar ba ta iya biyan bukatun kasashe 6 ba, kasar Amurka za ta nemi sanya takunkumin tattalin arziki ga kasar Iran ta kwamitin sulhu na M.D.D. a farkon wata mai zuwa.(Danladi)
|