An labarta ,cewa yanzu sassan da abun ya shafa na kasar Sin sun himmantu wajen binciken irin dafin da ake samu cikin magungunan gargajiya na kaksar Sin domin ba da tabbaci ga jama'a wajen shan irin wadannan magunguna lami-lafiya.
Madam She Jin, mataimakiyar ministan kiwon lafiya ta kasar Sin ta fayyace, cewa gwamnatin kasar Sin ta ware kudade don gina cibiyoyi da kafa dakunan gwaje-gwaje, inda kwararun da abun ya shafa suka yi nazari n musamman cikin tsanaki kan irin dafin dake cikin magungunan gargajiya na kasar Sin. Ban da wannan kuma, sassan da abun ya shafa na gwamnatin kasar su ma sun bukaci ma'aikatun harhada magungunan gargajiya da su yi bayani a rubuce kuma ba tare da rufa-rufa ba game da lokacin shan magani da kuma illar da zai iya yi ga masu shansa. ( Sani Wang )
|