An labarta, cewa yau Laraba, a nan Beijing, an yi bikin sauke karatu na kwas din horaswa ta kasa da kasa da bangaren gwamnatin kasar Sin ta shirya domin tallafa wa kasashe masu tasowa wajen horar da ma'aikata masu sa ido kan ingancin abinci.
Ma'aikata 32 daga kasar Albaniya da kuma kasar Cuba da dai sauran kasashe masu tasowa guda 21 sun shiga kwas din, wanda aka bude a ran 10 ga watan jiya. Kwararrun da abun ya shafa na kasar Sin sun bayyana wa wadannan ma'aikata fasahohin da kasar Sin suka samu wajen dudduba ingancin abinci; Sa'annan sun bayyana yadda kasar Amurka da kuma kungiyar tarayyar Turai suke bincike da kuma tabbatar da abinci na halitta da na canzawar kwayoyin halitta wato ' Gene'. ( Sani Wang )
|