Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-23 15:48:42    
' Yan makarantar sakandare na kasar Sin sun samu lambar yabo ta ruwa ta yara a Stokholm

cri

An gudanar da bikin mika lambar yabo ta ruwa ta yara manyan gobe ta Stokholm a shekarar 2006 ran 22 ga wata da dare. ' Yan makarantar sakandare guda 3 daga birnin Shanghai na kasar Sin sun yi alfaharin samun wannan lambar yabo ne a sanadiyyar kyakkyawan sakamakon bincike da suka samu wajen daidaita maganar gurbacewar ruwan koguna.

A wannan rana da dare, mai jiran gadon sarautar kasar Sweden Gimbiy Victoria ita kanta ce ta mika takardar shaidar samun lambar yabo bisa sunan Asusun Ruwa ta Stockholm ga wadannan 'yan makaranta guda 3, wadanda kuma suka samu kudin yabo da ya kai dola 5,000 da kuma wani kayan sassaka irin na lu'u-lu'u.

Bisa jagorancin malamansu ne, wadannan 'yan makaranta guda 3 suka soma yin nazarin fasahar farfado da halittun hanyoyin koguna a karshen shekarar 2004. Bisa namijin kokarin da suka yi tare, a karshe dai sun gabatar da wani shirin kyautata ingancin ruwan hanyoyin koguna madaidaita da kanana na birane. ( Sani Wang )