Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-23 10:12:55    
Kungiyar wasan taekwondo ta kasar Sin na zura ido kan taron wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing

cri

Kwanakin baya, an kawo karshen budaddiyar gasar kasa da kasa ta wasan taekwondo na kasar Sin, wadda aka shafe kwanaki 3 ana yinta a babban dakin wasannin motsa jiki na dalibai na Beijing. Wannan ne karo na farko da kasarmu ta shirya wannan gasa, wadda kuma ta samar da wata kyakkyawar dama ga 'yan wasan taekwondo na kasar Sin da na kasashen waje wajen share fage ga halartar taron wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing a shekarar 2008. ' Yan wasan taekwondo na mata na kasar Sin sun nuna rawar gani a gun gasar da aka yi a wannan gami. Wassu kwararru a fannin wasannin motsa jiki sun yi hasashen, cewa wadannan 'yan wasa mata na kasar Sin za su iya samun kyakkyawan sakamako a gun taron wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing a shekarar 2008.

' Yan wasa da kuma malaman koyarwa fiye da 180 daga kasar Sin, da yankin Taipei na kasar Sin, da kasashen Korea ta Kudu, da Jordan, da Iran, da Poland da kuma Fransa da dai sauransu sun halarci wannan gasa. Bayan da aka yi gasa cikin zazzafan hali, 'yan wasan kasar Sin sun kwashe dukannin lambobin zinariya guda 4 a fannin wasan mata, kuma ta kama matsayin farko a gun wannan gasa da samun lambobin zinariya guda 4, da lambobin azurfa guda 4 da kuma lambobin tagulla guda 5. Kuma nasara ce mafi kyau da kungiyar kasar Sin ta samu tun bayan da ta shiga gagaruman budaddun gasanni guda 4 na duniya. Kungiyar kasar Korea ta Kudu ta zo ta biyu da lambobin zinariya guda 2 da kuma lambobin azurfa guda 2 ; kuma kungiyar wasan yankin Taipei na kasar Sin ta samu lambobin tagulla guda 2.

Budaddiyar gasa ta kasar Sin, gagarumar budaddiyar gasa ce ta hudu ta duniya ta bayan budaddun gasanni na kasashen Iran, da Amurka da kuma Korea ta Kudu wadanda hadaddiyar kungiyar wasan taekwondo ta kasa da kasa ta amince da su. Babban mai koyar da 'yan wasan taekwondo na mata na kasar Sin Mr. Lu Xiudong ya furta, cewa: 'Lallai gasar nan da aka yi a wannan gami gasa ce mafi girman sikeli a cikin tarihin irin wannan wasa saboda kasashe da jihohi 15 kamar su kasar Korea ta Kudu, da kasar Vietnam da kuma yankin Taipei sun halarta, wadanda kuma suka mai da hankali sosai kan wannan gasar domin mayar da ita a matsayin wani gwaji ne da suka yi wajen lahartar taron wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing a shekarar 2008.'

Kungiyar yankin Taipei ta kasar Sin ta turo wassu nagartattun 'yan wasa zuwan nan Beijing domin halartar gasar. Daya daga cikinsu mai suna Zhu Muyan ya yi suna a duniya saboda ya zama lambawan a gun irin wannan wasa tsakanin maza masu nauyin jiki na kilo 58 a gun taron wasannin motsa jiki na Olympic na Aden da aka yi a shekarar 2004. Ban da wannan kuma ,' yar wasa mai suna Luo Wei ta kasar Sin, ita ma zakara ce a gun wasanin Olympic na Aden, kuma ta kara nuna kwarewa a gun gasar da aka yi a wannan gami har ta lallasa abokiyar karawarta. Ta yi farin ciki da fadin, cewa :

'Dukan 'yan wasanmu sun hada kansu sosai wajen yin gasa domin ganin tayar da tutar kasar mahaifa sama. Suna yin koyi da juna kuma suna taimakon juna'.

Mr. Zhao Lai, mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar wasan taekwondo ta kasar Sin ya fadi, cewa :

' A galibi dai, 'yan wasa maza da mata na kasar Sin dukansu sun nuna kyakkyawar halayya a gun gasa, musamman ma 'yan wasa maza sun samu babban ci gaba. Ya kamata mu yi koyi da kyawawan fasahohi daga 'yan wasa na ketare, ta yadda za mu cimma burin masu sha'awar wasan taekwando na kasar Sin a gun taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. ( Sani Wang )