Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-23 10:11:25    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki ( 17/08-23/08)

cri

Kungiyar wakilan kwamitin wasannin motsa jiki na Olympic na kasa da kasa dake karkashin jagorancin Mr. Hein Verbruggen, shugaban kwamitin daidaituwa na taron wasannin Olympic na 29 na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa, ran 15 ga watan nan, ta kammala ziyarar duba aiki ta kwanaki biyu a yankin Hongkong, inda ta gamsu da ganin aikin share fage da yankin yake yi na daukar nauyin gudanar da gasar tseren dawaki na taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Za a yi irin wannan gasa ne a filayen wasa guda biyu na Hongkong.

Kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing da karamar kungiyar daidaituwa ta masu sa kai na taron wasannin Olympic na Beijing sun hada kansu wajen shirya wani ' Taro kan aikin karbar masu sa kai na taron wasannin Olympic da taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing' a ran 18 ga watan nan a nan Beijing. Bisa shirin da aka tsara, an ce za a karbi masu sa kai da yawansu 70,000 na taron wasannin Olympic da kuma masu sa kai da yawansu ya kai 30,000 na taron wasannin Olympic na nakasassu, wadanda kuma za a karbi yawancinsu a nan Beijing yayin da za a karbi wassu daga mazaunan wurare daban daban na kasar Sin, da 'yan uwa na Hongkong da macao da Taiwan, da Sinawa mazauna kasashen ketare da kuma baki.

Ran 18 ga watan nan, an kafa rukunin farko na kungiyoi 18 na taron wasannin Olympic na Beijing. Wadannan kungiyoyi za su kula da aikin daidaita kashi 90 cikin 100 na matsalolin da za su wakana a cikin filaye da dakunan wasanni. A lokacin taron wasannin Olympic, 'yan wasa fiye da 10,000 da 'yan jarida fiye da 30,000, da dimbin shugabannin kasashe da na gwamnatoci da kuma dubban 'yan kallo za su taru a filaye da dakunan wasanni daban daban domin kallon wasanni.

Ran 20 ga wata, a birnin Qingdao na kasar Sin, an yi bikin bude gasar tseren kwale-kwale ta kasa da kasa ta Qingdao a shekarar 2006. ' Yan wasa fiye da 460 daga kasashe da jihohi 40 sun halarci gasar, wadda kuma ta zama wata gasa ce mafi girma da ake gudanar da ita a kasar Sin a cikin tarihi. Za a yi gasar tseren kwale-kwale ta taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 a nan birnin Qingdao.

Za a yi gasar cin kofin duniya ta 11 ta wasan kwallo mai laushi wato softball daga ran 27 ga watan nan zuwa ran 5 ga watan gobe a filin wasa na unguwar Fengtai ta birnin Beijing na kasar Sin.

An kawo karshen gasar cin kofin duniya ta 11 ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle na matasa a ran 20 ga wata da dare a nan Beijing. Kungiyar kasar Sin ta zo ta farko wajen samun lambobin yabo a gun gasar; Kungiyar kasar Kenya ta fi samun lambobon zinariya a gun gasar; Kuma kungiyar kasar Amurka tana biye da su. ( Sani Wang)