Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-22 20:27:05    
Rikici yana cin gaba a Kinshasa

cri
Sojojin tsaro da ke karkashin shugabancin shugaban kasar Congo(Kinshasa) Mr. Laurent-Desire Kabila da dakaru masu biyayya ga mataimakin shugaban kasar Mr. Jean-Pierre Bemba suna cin gaba da yin rikici da makamai a tsakaninsu a ran 22 ga wata, wadanda suka ta da rikici a cibiyar birin Kinshasa, hedkwatar kasar tun daga ran 20 ga wata da yamma.

Yanzu 'yan sandan kwantar da tarzoma da 'yan sandan kiyaye tsaron lafiyar al'umma masu yawa suna sarrafa manyan mahadar hanyoyi, sojojin tsaro suna kai samame ga wasu yankunan musamman. Ko da yake ana yin kazamin fada a Kinshasa, amma ana samar da ruwa da wutar lantarki yadda ya kamata, shi ya sa a galibi dai Sinawa fiye da dubu da ke zama a nan sun yi hakuri, suna cikin gida don jiran halin da ake ciki ya koma yadda ya kamata.

Sojojin gwamnatin kasar Congo(Kinshasa) ba su shiga cikin wannan rikici kai tsaye ba. Gwamnatin kasar Congo(Kinshasa) da sojan musamman na Majalisar Dinkin Duniya da kuma sojojin kiyaye zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Turai ba su ce kome ba kan wannan fada, ba a tabbatar da mutuwa da mutanen da suka jikata a sakamakon wannan rikici ba.(Tasallah)