Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-22 19:41:19    
Sojojin Nijeriya sun bindige dakaru 10

cri
A ran 21 ga wata, wani jami'in kasar Nijeriya ya bayar da labarin, cewa a ran 20 ga wata da dare, sojojin gwamnatin sun yi musanyan wuta da dakaru masu neman 'yancin kan Niger Delta na kungiyar MEND a kudancin jihar Bayelsa, inda aka bindige a kalla dakaru 10.

Kungiyar MEND ta yi nuni da cewa, mutanensu sun gamu da kwanton-baunar da sojojin gwamnatin suka kai musu, yayin da suke sakin wani mutum da aka yi garkuwa da shi.

Cikin watannin da suka wuce, an yi ta samun rahotannin sace mutane a kudancin kasar Nijeriya inda ke fitar da man fetur. Don haka, gwamnatin tarayya ta fara kai farmaki ga wadannan dakaru masu sace mutane a makon da ya gabata. Yanzu a Port Hacourt an riga an kama dakaru 160, kuma an tsare wasu 60 da ake zarginsu da aikata mummunan aiki na sace mutane.(Bello)