Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-22 17:19:35    
Ziyarar dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya na Henan

cri

Lardin Henan da ke tsakiyar kasar Sin yana daya daga cikin tushen al'adun gargajiya na kasar Sin. Ana samun tsoffin kayayyakin al'adu da na tarihi masu yawa a nan saboda dogon tarihinsa. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan kayayyakin gargajiya da aka samu a Henan ya zama na farko a cikin dukan lardunan kasar Sin, kuma dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya na Henan yana daya daga cikin manyan dakunan nune-nunen kayayyakin gargajiya guda 3 na kasar Sin. To, yanzu bari mu ziyarci wannan dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya.

Dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya na Henan yana a birnin Zhengzhou, babban birnin lardin Henan, shekarunsa ya kai fiye da 70, inda ake nuna kayayyakin gargajiya misalin miliyan 1 da dubu dari 3, yawansu ya kai kashi 1 cikin kashi 8 bisa na dukan kayayyakin gargajiya da ake ajiye cikin dakunan nune-nunen kayayyakin gargajiya a duk kasar Sin. Shugaban dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya na Henan Mr. Ding Fuli ya ce, ana ajiye kayayyakin gargajiya iri daban daban masu yawa a cikin dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya na Henan, a cikinsu kuma akwai wadanda ba safai ake samunsu ba. Ya ce, 'a cikin kayayyakin gargajiya da ake nunawa a cikin dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya na Henan, akwai wasu wadanda ba safai a kan gansu ba a cikin wasu sauran dakunan ajiye kayayyakin gargajiya, shi ya sa ma iya cewa, idan masu yawon shakatawa sun kawo wa Henan ziyara, amma ba su ziyarci dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya na Henan ba, to, za su yi da na sani.'

Mr. Ding ya kara da cewa, a cikin dukan kayayyakin gargajiya da ake ajiyewa a nan, kayayyakin tagulla sun fi nuna halin musamman. Kafin shekaru fiye da dubu 4, Sinawa sun fara narkar tagulla zuwa ruwa, kuma sun kera kayayyaki da shi, kayayyakin tagulla da Sinawa suka kera sun yi suna ne saboda nagarta da inganci da kuma fasaha.

Lardin Henan cibiya ce ta kasar Sin wajen siyasa da tattalin arziki tun daga karni na 21 kafin haihuwar Annabi Isa zuwa shekarar 475 kafin haihuwar Annabi Isa, shi ya sa an tono kayayyakin tagulla da yawa da karkashin kasa a nan, an ajiye wasu daga cikinsu a cikin dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya na Henan. Wadannan kayayyakin tagulla sun nuna al'adun kayayyakin tagulla na kasar Sin.

Yanzu za mu gabatar muku da wasu daga cikin wadannan kayayyakin tagulla masu daraja, kamar buta mai suna Lian He, wani shahararren karamin kayan tagulla, wadda tsayinta ya kai santimita 12 kawai. Shekarunta ya kai fiye da 2500.

Sa'an nan kuma, takobin bakin karfe tare da tagulla a cikinsa shi ma ya yi suna kwarai, saboda har zuwa yanzu shi kaya ne mafi tsufa da aka yi da karfe a kasar Sin.

Ban da wannan kuma, a cikin dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya na Henan akwai wasu sauran kayayyaki da suka zama na farko a duk kasar Sin.

Sarewar da aka yi da kashin kafar namun daji kayan kida ne mafi tsufa da ya zuwa yanzu aka gano a kasar Sin, shekarunta ya kai misalin dubu 8. amma tana nan sumul garau. Abin mamaki shi ne wannan sarewa ta iya aiki, ta iya rera wakoki masu dadin ji har zuwa yanzu, ba safai a kan ji irin wannan labari ba a cikin tarihin kide-kide na kasa da kasa.

Masu yawon shakatawa na gida da na waje masu yawa su kan ziyarci dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya na Henan saboda kayayyakin gargajiya da ke cikinsa, wadanda ke nuna al'adun kasar Sin sosai. Madam Kim Min R, wata malamar koyarwa da ta fito daga kasar Korea ta Kudu, ta jagoranci dalibanta wajen ganin wadannan kayayyakin gargajiya masu daraja, ta ce, 'kayayyakin gargajiya da ake ajiye a cikin dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya na Henan sun ba da babban taimako ga yara wajen yin karatu, nan gaba zan sake ziyarar shi in ina da dama.'

Ba kayayyakin gargajiya kawai ba, masu yawon shakatawa sun iya sauraren kide-kiden gargajiya na kasar Sin a nan. Makada sun yi amfani da kayayyakin kida da aka kera kamar irin kayayyakin kida na gargajiya na kasar Sin, sun samar da kide-kide masu dadin ji.(Tasallah)