Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-22 17:15:45    
Dakin nune-nunen kayayyakin fasaha na kasar Sin

cri

Dakin nune-nunen kayayyakin fasaha na kasar Sin dakin nune-nunen kayayyakin fasaha ne mafi girma a duk kasar Sin, shi ne daya daga cikin manyan gine-gine 10 da aka gina su don murnar cikon shekaru 10 da kafuwar Jamhuriyar jama'ar kasar Sin, mazauninsa na arewa maso gabashin fadar sarakuna ta kasar Sin wato Forbidden City a birnin Beijing, hedkwatar kasar, wanda ke dora muhimmanci kan nuna da ajiye da kuma nazarin kayayyakin da masu fasaha na zamani da zamanin kusa da na yanzu na kasar Sin, sa'an nan kuma wuri ne na matsayin koli wajen nuna kayayyakin fasaha na kasar Sin, shi ya sa ya ba da babban tasiri a rukunin fasaha.

An fara gina babban ginin wannan dakin nune-nunen kayayyakin fasaha kamar irin dakin gargajiya na kasar Sin tun daga shekarar 1958, an gama gina shi a shekarar 1962. Dakin nune-nunen kayayyakin fasaha na kasar Sin ya nuna salon kabilu na gargajiya sosai. Shehun malami mai ilmin gine-gine Mr. Dai Nianci ne ya jagoranci zana wannan dakin nune-nunen kayayyakin fasaha, ya koyi salon gine-gine na kogon dutse na Mo Gao Ku da ke Tunhuang, ya ci nasarar hada salon gine-gine na zamani da na kabilu gaba daya wajen zana wannan dakin nune-nunen kayayyakin fasaha. Fadin dakin nune-nunen kayayyakin fasahar nan ya kai murabba'in mita misalin dubu 30, fadin babban gininsa ya kai murabba'in mita dubu 17 da 51, jimlar fadin dakunan nune-nunen kayayyakin fasaha guda 14 ta kai murabba'in mita dubu 6.

Yanzu ana ajiye zane-zane iri na kasar Sin da na kasashen yamma da sassaka iri daban daban fiye da dubu 10, a cikinsu kuma akwai nagartattun kayayyakin da kwararru masu ilmin zane-zane na zamani da zamani na kusa da na yanzu kamar su Shi Tao da Ren Bonian da Wu Changshuo da XU Beihong, da kuma wasu masu zane-zane na zamani suka samar da su. Ban da wannan kuma, a kan shirya gagaruman nune-nunen kayayyakin fasaha da yawa a nan a ko wace shekara.(Tasallah)