Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-22 15:41:33    
Shan taba na da saukin kamuwa da ciwon sukari

cri

Yanzu za mu soma gabatar muku da labarin da muka shirya muku. Bisa rahoton bincike da 'mujallar ilmin aikin likita ta kasar Birtaniya' ta bayar a kwanan baya, an ce, ba ciwon zuciya da ciwon kansa kawai ba, mai yiwuwa ne shan taba zai haifar da ciwon sukari. Duk da mutane su sha taba da kansu, ko kuma wadanda ba su sha taba ba, amma suna zama tsakanin masu shan taba kullun, an tilasta musu shan taba.

Wata cibiyar nazarin ilmin aikin likita ta Birmingham ta kasar Amurka ta yi bincike kan halin da mutane kimanin 4500 suke ciki a fannin lafiyarsu a biranen Birmingham da Chicago da dai sauransu a shekarar 1985 da ta 2000. Sakamakon da aka samu ya nuna cewa, tun daga shekarar 1985 zuwa ta 2000, masu shan taba da yawansu ya kai kashi 22 cikin dari sun fito da alamar kamuwa da ciwon sukari. Dalilin da ya sa kamuwa da ciwon sukari shi ne jikin mutum bai iya samar da wani abu mai suna insulin a bakin Turawa ba, wanda ya iya kyautata sukari a cikin jinin mutum.

Ban da wannan kuma, mutanen da ba su taba shan taba ba, amma su kan kullun zama tsakanin masu shan taba su ma sun fito da alamar kamuwa da ciwon sukari, yawansu ya kai misalin kashi 17 cikin dari, wadanda suka taba shan taba, amma daga baya ba su ci gaba da shan taba ba da yawansu ya kai misalin kashi 14 cikin dari sun fito da alamar kamuwa da ciwon sukari. Mutanen da ba su taba shan taba ba, kuma ba su zama tsakanin masu shan taba ba da yawasu ya kai misalin kashi 11.5 cikin dari sun fito da irin wannan alama.

Rahoton ya yi bayanin cewa, mai yiwuwa ne dafin da aka samu a lokacin da taba ya kone zai tattara a cikin wani kayan ciki na mutum, wanda ya samar da insulin, amma ana bukatar cin gaba da yin nazari kan wannan bayani.

Sa'an nan kuma, rahoton bincike ya nuna cewa, mai yiwuwa ne barazananr da yin zama tsakanin masu shan taba ya kawo wa mutane ta fi wadda aka kiyasta. Hayakin da aka samar da shi a lokacin shan taba ya sanyayu a cikin iska, ya kuma canja kansa, a sakamakon haka, hayakin da mutane suka numfashi ya fi kunshe da dafi, in an kwatanta shi da wanda masu shan taba suka numfashi kai tsaye.(Tasallah)