Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-22 15:38:05    
Kamfanonin kasar Sin sun yi nazari da samar da sababbin magungunan shawo kan zazzabin ciwon sauro ga kasashen Afirka

cri

A watan Yuni na bana a yayin da firayin ministan kasar Sin Wen Jiaobao ya kai ziyara a kasashe 7 na Afirka, ya ba su wata kyauta mai suna 'Ketaifu'. To, wannan shi ne sabon magani da kamfanonin kasar Sin suka yi nazari da samar da shi domin shawo kan zazzabin cizon sauro a kasashen Afirka.

Rukunin Huali, wanda hedkwatarsa yake birnin Hangzhou da ke gabashin kasar Sin ne, ya samar da wannan sabon magani. Kakakin rukunin Huali ya gaya mana cewa, a halin yanzu dai, rukuninsa yana da magunguna iri daban daban na 'Ketaifu', haka kuma ya riga ya yi rajista da sayar da magungunan 'Ketaifu' a kasashen Afirka da yankunan da ke kudu maso gabashin Asiya da yawansu ya kai 28.

A halin yanzu dai, ana aikin gwaji da yin rajistar magungunan 'Ketaifu' a duk duniya, haka kuma kungiyar kiwon lafiya ta duniya tana bincike a kan magungunan.

A matsayin wata cuta mai yaduwa, zazzabin cizon sauro yana yaduwa sosai a yankunan da ke kudancin hamadar Sahara a halin yanzu. Bisa kididdigar da kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta bayar, an ce, a ko wace shekara, yawan mutane da suke mutuwa a sakamakon zazzabin ciwon sauro ya kai kusan miliyan 500, haka kuma zazzabin ciwon sauro yana yaduwa a kasashe fiye da 100. A kasashen Afirka kuma, mutane kimanin miliyan 500 sun mutu a sakamakon zazzabin ciwon sauro a ko wace shekara, rabin daga cikinsu su yara ne.

Ya zuwa yanzu, manyan kamfanoni uku da ke samar da kuma fitar da magungunan shawo kan zazzabin ciwon sauro su ne rukunin Huali na Chongqing da rukuni Kunming da rukuni Guilin.

Rukuni Huali ya zama na farko da kamfanin kasar Sin ya yi nazari da samar da magungunan shawo kan zazzabin ciwon sauro kuma ya fitar da su zuwa kasashen Afirka, ya zuwa yanzu tarihinsa ya kai shekaru 12.

Daga shekarar 2004, rukunin Huali ya riga ya kafa reshen kamfaninsa ko ofishin sayar da magungunansa a kasashen Kenya da Tanzania da Faransa da Nijeriya da Uganda da dai sauran kasashe ko yankuna.

A watan Afrilu na shekarar 2006, rukuni Huali ya kafa cibiyar jigilar kayayyaki a kasar Kenya, to, wannan ya share fage ga kamfanin da ya samar da magungunan 'Ketaifu' a yankunan Afirka, haka kuma, wannan ya rage kudin jigilar magungunan.

A sa'i daya kuma, rukuni Huali ya bayar da kudin kyauta a cibiyar nazarin fasahar asibitoci a kasar Kenya, ta yadda yana son nuna goyon baya ga ba da ilmi da horar da kwararru a fannin likitanci da magunguna a wurin.(Danladi)