A ran 21 ga wata a birnin Tehran, shugaban addini na kasar Iran Ali Khamenei ya bayyana cewa, kasar Iran za ta ci gaba da shirinta na makamashin nukiliya.
A ran nan Mr Khamenei ya yi wani jawabi a gidan TV na kasar Iran cewa, kasar Iran za ta ci gaba da gudanar da shirinta na amfani da makamashin nukiliya.
A ran nan a birnin Pretoria na kasar Afirka ta kudu, ministan harkokin waje na kasar Iran Manouchehr Mottaki, wanda yake ziyarar aiki a kasar, ya bayyana cewa, kasar Iran ta riga ta shirya sosai domin ba da amsa ga shirin da ministocin harkokin waje 6 suka gabatar. Ya ci gaba da cewa, Iran tana fata za a warwae matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar yin shawarwari, kamata ya yi a giramama ikon da kasar Iran take da shi wajen amfani da makamashin nukiliya.(Danladi)
|