Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-21 16:36:28    
kasar Sin tana yin kokari domin rage yawan mata masu ciki da suke mutuwa a yankuna masu fama da talauci na kasar

cri

Yawan mutuwar mata masu ciki wani muhimmin ma'auni ne na bunkasuwar zamantakewar al'umma da kuma wayewar kai na wata kasa ko wata shiyya. Kasar Sin wata kasa ce wadda fadin yankunanta na da girma sosai, kuma ba a iya bunkasa wurare daban daban na kasar cikin daidaici ba, shi ya sa a wasu yankuna masu fama da talauci na tsakiya da yammacin kasar Sin, yawan mata masu ciki da suke mutuwa ya yi yawa. A shekara ta 2000, gwamnatin kasar Sin ta fara wani aiki a yankunan wanda makasudinsa shi ne rage yawan mutuwar mata masu ciki. Ya zuwa yanzu an riga an samu sakamako mai kyau sosai. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan kokarin da ake yi don rage yawan mutuwar mata masu ciki a yankunan.

Gundumar Muchuan wata gunduma ce da ke kan duwatsu masu yawa a kudancin jihar Sichuan, wadda take fama da talauci mai tsanani. Madam Li Yunzhen tana da zama a cikin wani kauye da ke hannun gundumar. Yanzu shekarunta da haihuwa ya kai 40, tun shekara ta 1990, bi da bi ne ta samu ciki har sau hudu. Sabo da babu kudi, har kullum ta kan haifu a gida, amma yaranta guda uku sun mutu sakamakon haihuwa, kuma sau da dama ita kanta ta kusan tafi gidan gaskiya. A shekara ta 2005, ta sake samun ciki, bayan da likitan kauyen ya yi mata bincike, ya gaya mata cewa, cikinta ya jirkice, shi ya sa tilas ne ta je asibiti idan lokacin haihuwa ya yi. Li Yunzhen ta nuna damuwa sosai ga wannan, ta ce,

"Likitoci na kauyenmu sun bukaci in je asibiti don haihuwa, ba ni da kudi, ba yadda za a yi sai na haifu a gida. Amma likitocin ba su yarda ba, sun gaya mini cewa, idan ina da kudi, sai na ba su, in ba ni da kudi, sai na bi bashi, ba tilas ba ne na biya dukkan kudi sau daya. Daga baya kuma na haifu a asibiti, na yi musu godiya sosai, sabo da in ba haka ba, tabbas ne 'yata za ta mutu. "

Bisa manufofin wurin, idan mata masu fama da talauci kamar Li Yunzhen sun je asibiti don haihuwa, to za su iya samun alawus daga gwamnatin wurin, kuma ba tilas ba ne suka biya dukkan kudaden da suka kashe sau daya.

Babban daraktan gundumar Muchuan Ye Sanqiang ya bayyana cewa, bayan shekara ta 2000, an riga an bayar da taimako ga mata masu ciki da suke fama da talauci fiye da 1300 gaba daya, kuma yawan kudin da aka samar ya kai yuan dubu 190. Sabo da wadannan taimako da aka bayar, mata masu ciki da yawansu ya kai kashi 70 cikin dari sun je asibiti don haihuwa, sabo da haka yawan mutuwar mata masu ciki na gundumar Muchuan na shekara ta 2005 ya kai rubu'in na shekara ta 1999.

Ban da gundumar Muchuan, gundumomin Ebian da Jinkouhe da Mabian da dai sauransu da ke makwabtaka da ita sun fara ayyukan rage yawan mutuwar mata masu ciki. Musamman ma a wasu yankunan da aka fi samun 'yan kananan kabilun Sin da yawa da kuma wadanda suke fama da talauci mafi tsanani, al'adun gargajiya na da da kuma hanyoyin haihuwa na baya suna takawa rawa. Sabo da haka hukumomin da abin ya shafa sun koyar da ilmin kiwon lafiya don canja ra'ayoyin fararen hula kan haihuwa. Alal misali, wata al'adar gargajiya ta kabilar Yi ita ce tilas ne a haifi yara a gida, ba a karbi yaran da aka haife su a waje ba. Amma bayan da aka yi furofaganda a cikin shekarun nan da suka gabata, yawancin 'yan kabilar Yi sun canja ra'ayinsu na baya kan haihuwa. Madam Tian Qiong, wata mace na kabilar da ta haihu a asibiti ta gaya wa wakilinmu cewa,

"haihuwar yara a asibiti na da kyau sosai. Sabo da kayayyakin asibiti suna da kyau, shi ya sa hankali ke kwanciya sosai idan an haifi yara a nan."

Bisa labarin da muka samu, an ce, gwamnatin kasar Sin ta fara ayyukan rage yawan mutuwar mata masu ciki a shekara ta 2000, ya zuwa yanzu ana yin ayyukan a gundumomi kusan 100, wato ya shafi kusan dukkan yankunan tsakiya da yammacin kasar Sin wadanda tattalin arzikinsu ya yi baya. Kakakin ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin Mao Qun'an ya bayyana cewa,

"ya zuwa karshen shekara ta 2005, an aiwatar da ayyukan rage yawan mutuwar mata masu ciki a jihohi 23 na kasar Sin, kuma yawan mutuwar mata masu ciki ya ragu zuwa kashi 56.4 ciki kashi dubu 100, wato ke nan ya ragu da kashi 25.8 cikin dari bisa na shekara ta 2001."

Bugu da kari kuma Mr. Mao ya ce, za a ci gaba da aiwatar da ayyukan rage yawan mutuwar mata masu ciki a duk kasar Sin. A waje daya kuma, za a kafa tsarin gudanarwa mai kyau a wurare daban daban na Sin don lura da lafiyar mata masu ciki sosai.(Kande Gao)