Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-21 16:33:39    
Takaitaccen bayani kan kananan kabilun Sin

cri

Tun fil azal, kasar Sin wata dinkakkiyar kasa ce mai kabilu da yawa. Bayan kafuwar kasar Sin, yawan kabilun da gwamnatin kasar Sin ta tabbatar ya kai 56. Ban da kabilar Han, yawan mutanen sauran kabilu 55 ya yi kadan idan an kwatanta shi da na kabilar Han, sabo da haka, a kan kira su kananan kabilu.

Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da kuma gwamnatin kasar sun tsara manofofi da dama da suka dace da halin musamman da Sin ke ciki domin warware batutuwan kabilun kasar Sin, wato manufar zaman daidai wa daida tsakanin kabilu da manufar hadin gwiwa tsakanin kabilu da manufar cin gashin kan kananan kabilu da kuma manufar samun bunkasuwa da wadata tare ta kabilu daban daban. Ban da wannan kuma, bisa ra'ayin yawancin 'yan kananan kabilu, gwamnatin kasar Sin ta dauki dabaru daban daban wajen yin gyare-gyaren dimokuradiyya a yankunan kananan kabilu wanda aka sa aya gare su a karshen shekaru 50 na karnin da ya gabata.

Ko da yake yawan 'yan kananan kabilun Sin ya yi karanci, amma suna barbazuwa a ko ina. An fi samun 'yan kananan kabilu a jihohin Mongolia ta gida da Xinjiang da Ningxia da Guangxi da Tibet da Yunnan da Guizhou da sauransu. A ciki, yawan kananan kabilu da ke cikin jihar Yunnan ya fi yawa, wato ya kai 25.

Tsarin gudanar da harkokin kananan kabilu da kansu wani babbar manufa ce da gwamnatin kasar Sin ke dauka bisa halin da take ciki, haka kuma shi wani muhimmin tsarin siyasa ne na kasar Sin. Ya zuwa karshen shekara ta 1998. kasar Sin ta kafa jihohin kananan kabilu masu cin gashin kai 15 gaba daya. Haka kuma a cikin kananan kabilu 55, kabilu 44 sun kafa wuraren cin gashin kansu.

Bugu da kari kuma, bayan kafuwar kasar Sin, har kullum gwamnatin Sin tana tsayawa kan bin manufar zaman daidai wa daida tsakanin kabilu daban daban da kuma ta daidai wa daida kan harsunan kabilu, sabo da haka an bayar da tabbaci ga yin amfani da harsunan kananan kabilu da bunkasuwarsu.(Kande Gao)