Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a ran 20 ga watan nan a birnin Alkahira , hedkwatar kasar Masar , ministocin harkokin waje da wakilan kasashen Larabawa sun yi taro , inda suka yi alkawarin ba da taimako ga kasar Lebanon don farfado da kasar .
A wannan rana ministocin da wakilan kasashe mambobi 22 na Kungiyar tarayyar kasashen Larabawa sun halarci taron kan matsalar Lebanon . Mahalartan taron sun yi na'am da kai gundumuwa ga kasar Lebanon wadda kasar Isra'ila ta kaiwa farmaki sau da yawa a yankin . Za a sanar da hakikanin shirin kai agaji a taron ministocin kudi na kasashen Larabawa a watan Satumba .
Mahalartan sun kuma bayar da sanarwa , inda suka la'anci kasar Isra'ila saboda ta taka kuduri mai lambar 1701 na Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zartas a ran 19 ga watan Agusta . (Ado)
|