A ran 18 ga wata, madam Marie Heuze, kakakin ofishin M.D.D. da ke Geneva ta ce, rundunar soja ta wucin gadi ta M.D.D. da ke kasar Lebanon ta amince da cewa, an riga an fara janye sojojin Isra'ila daga yankunan kudancin kasar Lebanon tun daga ran 17 ga wata, a sa'i daya kuma, dakarun gwamnatin kasar Lebanon sun shiga wadannan yankuna.
Wannan kakaki ta ce, tun daga ran 17 ga wata ne aka soma janye sojojin Isra'ila daga yankunan kudancin Lebanon. A wannan rana kuma, dakaru masu dimbin yawa na gwamnatin Lebanon sun isa birnin Tyre da ke bakin teku a kudu maso yammacin Lebanon. Sannan kuma, a karkarshin taimakon rundunar soja ta M.D.D. da ke Lebanon, sun shiga wadannan yankuna. Yanzu, rukunin masu kawar da nakiyoyi na kasar Sin suna share nakiyoyi daga wadannan yankunan da ke kudancin Lebanon.
Bugu da kari kuma, a ran 17 ga wata a hedkwatar M.D.D. da ke birnin New York, Mark Mallock Brown, zaunannen mataimakin babban sakataren M.D.D. ya yi kira ga kasashen membobin M.D.D. da su samar da sojoji ga rundunar soja ta wucin gadi ta M.D.D. da ke Lebanon cikin gaggawa domin kara karfin wannan rundunar soja ta M.D.D. (Sanusi Chen)
|