Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-18 21:31:06    
Za a gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin jihar Tibet ta hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar Sin

cri

A ran 1 ga watan Yuli na shekarar nan, an fara aiki da hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar Sin gadan gadan, wadda aka shimfida a kan tsaunuka mafi tsayi a duniya. Ba ma kawai jama'ar jihar Tibet za su ci gajiyar wannan hanyar jirgin kasa wajen yin tafiye-tafiyensu cikin sauki sosai ba, har ma za su sami babbar dama wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin jihar Tibet.

Tsoho Duojiewanzha, wani makiyayi ne da ke zama a wani wuri mai suna Naqu, da ke a arewacin jihar Tibet. An kyautata zaman rayuwar duk iyalinsa ta hanyar shimfida hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar. Iyalinsa 7 suna kiwon shanu iri na Tibet guda 40 da awaki sama da 100. A lokacin da ma'aikata ke yin aikin shimfida hanyar jirgin kasa a wuri da ke dab da gidansa, sai tsohon nan ya kafa tanti a wurin inda yake sayar da kayan abinci kamar taliya da keke da kuma sauransu. Sauran iyalinsa kuma suka shiga aikin gadin hanyar jirgin kasa, ta haka suka sami kudin shiga mai yawa. Tshon nan ya bayyana cewa, "yanzu, ina son ci gaba da sayar da kayayyaki ta hanyar jirgin kasa. Bayan kaddamar da hanyar, zan dauki jirgjin kasa zan je birnin Ge'ermu, inda zan sayar da fatun shahu da na awaki da gashin tumaki da ake samu a kauyenmu a can. Sa'an nan zan komo da kayan masarufi gida don sayar da su ga mutanen kauyenmu."

Masanan ilmin tattalin arziki sun nuna cewa, ba ma kawai za a kara kyautata halin da ake ciki a jihar Tibet a fannin zirga-zirga da sufuri, ta hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jitar Tibet ba, har ma za a gaggauta bunkasuwar harkokin yawon shakatawa a jihar Tibet, kuma za a gaggauta raya ma'adinai a jihar.

Madam Liang Yuan, mataimakiyar manajar kamfanin yawon shakatawar kasa da kasa na Hong Kong ta bayyana cewa, "akwai fa'idoji guda uku idan an yi amfani da jirgin kasa zuwa jihar Tibet. Na daya, tikitin jirgin kasa yana da araha sosai idan an kwatanta shi da na jirgin sama. Na biyu, za a iya sabawa da shan iska mai kyau wadda ba ta da yawa a tsaunuka sannu a hankali, ba kamar yadda ake yi cikin jirgin sama ba. Na uku, za a iya more ido da ni'imatattun wurare da ke bakin sashen hanyar jirgin kasa da ya hada birnin Xijing da birnin Lhasa. "

Malam Zhanuo, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta jihar Tibet yana ganin cewa, bayan da aka kaddamar da hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet, yawan mutane da ke iya yin amfani da jirgin kasa zuwa jihar Tibet zai kai kimanin 4,000 a ko wace rana. Ta haka masu yawon shakatawa da ke zuwa jihar Tibet ma za su karu sosai.

Ban da wannan kuma za a gaggauta bunkasuwar harkokin ciniki a tsakanin kasashen Sin da Nepal da Indiya da kuma sauran kasashen kudancin Asiya, ta hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar Sin. Malam Wang Deyuan, mataimakin shugaban sashen nazarin harkokin tattalin arziki na cibiyar nazarin ilmin zaman rayuwar yau da kullum ta jihar Tibet ya bayyana cewa, "bayan da aka fara aiki da hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar Sin, za a yi jigilar kayayyaki zuwa birnin Lhasa, fadar gwamnatin jihar Tibet daga sauran wurare na kasar da sauki, kuma cikin sauri. Ko shakka babu, yawan kayayyaki da kasar Sin ke fitar zuwa kasashen waje ta hanyar nan, zai karu sosai. Ta haka, nan da 'yan shekaru masu zuwa, jihar Tibet za ta sami ci gaba da sauri, wajen bunkasa harkokin cinikin waje. Wannan hanyar jirgin kasa za ta zama wata hanya ce da ake bi wajen fitar da kayayyakin kasar Sin zuwa kasashen kudancin Asiya." (Halilu)