Ran 5 ga watan Mayu na kalandar kasar Sin ranar bikin duanwu ne. Cikin shekaru fiye da 2000 da suka wuce, bikin Duanwu kullum ya zama wani kyakkyawan biki ne ga kabilu da yawa na kasar Sin wajen kyautatta lafiyar jiki da yin rigakafi da warkar da cututuka da kawar da abubuwa masu dafi.
Ya kasance da bayanoni da yawa wadanda suka sha bambam game da mafarin bikin Duanwu, wasu sun bayyana cewa, bikin Duanwu ya faru ne daga al'adar lokacin rani ta zamanin da, wasu kuma suna ganin cewa, ya faru ne sabo da girmamawar da mutanen da ke kwarin kogin Yangtse na zamanin da ke nuna wa dodon Totem, amma galiban mutane suna ganin cewa, ana yin bikin Duanwu ne musamman domin tunawa da Qu Yuan, mawaki mai kishin kasa na zamanin da. Qu Yuan ya yi zaman rayuwarsa ne a karni na 3 na kafin haihuwar Annabi Isa alaihisallam a kasar Chu na lokacin yake-yaken sarakuna na Zhanguo, bayan da wata kasar abokan gaba ta mamaye kasar mahaifarsa, ya ji haushi sosai har ya tsunduma cikin ruwan kogin Guluo ya mutu, ran nan kuwa ran 5 ga watan Mayu na kalandar kasar Sin ne.
Daga baya kuma, a wannan rana ta ko wace shekara, domin tunawa da halin kirki na Qu Yuan, mutane sukan rataye jakunkuna masu kamshi, da cin wani irin abinci da ake kira Zongzi, da yin tseren kwale-kwale. An riga an shafe shekaru fiye da 2000 ana yin irin wadannan aikace-aikace.
Cikin shekaru fiye da dubu da suka wuce, halin kirki na kishin kasa na Qu Yuan ya burge mutane sosai, mutanen kasar Sin suna yin tseren kwale-kwale da cin abinci mai suna Zongzi a ranar bikin Duanwu ne musamman domin tunawa da Qu Yuan, har ya zama wani bikin duk al'umman kasar Sin.
Ban da abinci kuma, ya kasance da al'adar jama'a ta yin ado masu halin musamman a gun bikin Duanwu. A wannan rana, kowane iyali yakan rataya wata irin ciyawar da ake kira Mugwort da ta Cattail a bakin kofarsa domin yin rigakafi da kawar da ciwace- ciwace. Kuma akan yi gagaruman bukukuwan tsere-tseren kwale-kwale a bakin kogi ko tafki, kuma an buga ganguna da kuge, da yin kirarin farin ciki a kan kwale-kwale.
To, jama'a masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na "Me ka sani game da kasar Sin" daga nan S.H. na R.K.S.(Umaru)
|