Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-17 11:06:10    
Kungiyar SADC ta gaggauta aikin bunkasa tattalin arziki bai daya

cri

An rufe taron kwamitin ministocin Gamayyar raya kudancin Afirka wato kungiyar SADC na yini 2 a birnin Maseru, hedkwatar kasar Lesotho a ran 16 ga wata, inda kwamitin ministoci ya gabatar da manyan makaisudan bunkasuwa 5, wadanda ya kamata kasashen gamayyar su yi la'akari da su a gaban kome don gaggauta aikin bunkasa yanki bai daya.

A gun taron ganawa da manema labaru da aka yi a ran nan, sabon babban sakataren kwamitin ministocin kungiyar SADC kuma ministan kudi da shirye-shiryen bunkasuwa na kasar Lesotho Mr. Timothy Thahane ya bayyana cewa, a cikin shekarar da ta gabata, kudancin Afirka ya sami ci gaba sosai a fannonin siyasa da tattalin arziki. A fannin siyasa, an yi babban zabe ta hanyar dimokuradiyya a kasar Congo(Kinshasa) a karshen watan Yuli na shekarar da muke ciki, wanda karo na farko ne da aka yi a wannan kasa har tsawon shekaru 40. A fannin tattalin arziki kuma, ko da yake yana kasancewa da bambanci a tsakanin kasashe mambobin kungiyar, amma matsakaicin yawan karuwar tattalin arziki na wannan yanki na shekarar 2005 ya kai kashi 5 cikin dari, kuma an kiyasta cewa, wannan adadi zai kai kashi 6 cikin dari a shekarar da muke ciki. Ya kara da cewa, yankin da kungiyar SADC ke ciki yanki ne da aka fi samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, in an kwatanta shi da sauran yankunan Afirka, a sakamakon haka an samar da sharadi mai kyau wajen gaggauta aikin bunkasuwa yanki bai daya.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, a gun taron kwamitin ministocin kungiyar SADC da aka yi a wannan shekara, an dora muhimmanci kan yin tattaunawa kan yadda za a kyautata manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni da kuma cimma makasudin muhimman tsare-tsare na bunkasuwa yanki bai daya, bisa yarjejeniyar ciniki ta yanzu, wato za a kafa yankin ciniki maras shinge a shekarar 2008, za a kafa kungiyar tarayyar kwastan ta kungiyar SADC a shekarar 2010, za a kafa kasuwar tarayya ta kungiyar SADC a shekarar 2015, za a kuma kafa kungiyar tarayyar kudi ta kudancin Afirka a shekarar 2016, sa'an nan kuma, za a yi amfani da kudi iri daya a wannan yanki a shekarar 2018.

Mr. Thahane ya nuna cewa, kungiyar SADC tana kunshe da mambobi 14, tana da hukumomi da yawa, amma 'yan kwadago da albarkatu sun yi kalilan, sa'an nan kuma, ana bukatar cimma wadannan makasudai cikin gaggawa, saboda haka, kwamitin nan ya gabatar da manyan makaisudan bunkasuwa 5, wadanda ya kamata kasashen kudancin Afirka su yi la'akari da su a gaban kome don gaggauta aikin bunkasa yanki bai daya.

A gun taron ganawa da manema labaru da aka yi, sakataren zartaswa na kungiyar SADC Mr. Tomaz Augusto Salomao ya yi bayani kan wadannan manyan makasudan bunkasuwa 5. Na farko shi ne tabbatar da zaman lafiya da tsaron kai da kuma kwanciyar hankali na siyasa, wanda sharadi na farko ne wajen daidaita kalubale iri daban daban da wannan yanki ke fuskanta, da kuma tabbatar da samun bunkasuwa da kawar da talauci da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a. Na biyu shi ne ingiza yin ciniki ba tare da shige ba da kuma raya tattalin arziki bai daya, don share fage wajen kafa yankin ciniki maras shinge da kuma aiwatar da manufofin bai daya na tattalin arziki daga manyan fannoni. Na uku shi ne kara yin muhimman ayyuka da kyautata tsarin zirga-zirga na hanyoyi da warware matsalar karancin makamashi, don samar da sharuda masu sauki wajen yin cudanyar 'yan kwadago da kayayyaki ba tare da shinge ba a wannan yanki, ta yadda za a kara karfin takara na wannan yanki. Na hudu shi ne daga matsayin zaman rayuwar jama'ar wannan yanki da mai da hankali kan samar da isasshen abinci da matsalar ciwon cutar AIDS. Na biyar shi ne karfafa bunkasuwar kimiyya da fasaha da kuma horar da 'yan kwadago, da daga matsayin hadin gwiwar fasaha, ta yadda za a hada karfin kimiyya da fasaha na kasa da kasa na wannan yanki, a sakamakon haka kasashen da suke baya-baya ne a fannin kimiyya da fasaha za su ci riba.

Ban da wannan kuma, Mr. Thahane ya fayyace wa kafofin yada labaru cewa, don gaggauta aikin raya tattalin arziki bai daya, kwamitin ministoci ya yarda da kafa wata kungiyar musamman, wadda ke kula da ayyukan share fage wajen kafa kungiyar tarayyar kwastan ta kungiyar SADC. Ya kuma yarda da mika yarjejeniyar kudi da ciniki ga taron shugabanni na kungiyar SADC da za a bude a ran 17 ga wata don zartas da ita da kuma rattaba hannu a kanta.(Tasallah)