 A kwanan baya, kasar Sin ta buga littafin "Zababbun Bayanai na Jiang Zeming". Jiang Zeming, tsohon shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin tsakiya na rundunar soja ta 'yanttar da jama'ar kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. A cikin bayanan da aka zaba, an yaba wa tunani da matakan mulkin kasar Sin da tsofaffin shugabannin kasar Sin suka dauka. A ran 15 ga wata, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya kira gaggarumin taro a nan birnin Beijing, inda aka yi kira ga jama'ar kasar Sin da su yi koyi da tunanin Zababbun Bayanai na Jiang Zemin. A bayyane ne kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na yanzu ya bayyana cewa, zai ci gaba da bin tunanin tsofaffin shugabannin kasar Sin da matakan da suka dauka.
Tun daga shekarar 1989 zuwa shekara ta 2004 ne Jiang Zemin ya hau kan mukamin mulkin kasar Sin. A cikin shekaru 13 da yake kan mukaminsa, halin da ake ciki a duk fadin duniya ya samu sauye-sauye sosai, kasar Sin ma ta gamu da matsaloli da yawa lokacin da take bin manufar bude kofa ga kasashen waje da yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arzikinta. An bayyana cewa, lokacin da ake tsara wadannan zababbun bayanai, Jiang Zemin ya dudduba kowane bayani da kansa filla filla.

Litattafan Zababbun Bayanai na Jiang Zemin da aka wallafa sun jawo hankulan jama'ar kasar Sin sosai. A yawancin kantunan sayar da litattafai na Beijing da na sauran wuraren kasar Sin, an sa wadannan litattafai a kan wurin da ya fi jawo hankulan mutane. Mutane masu dimbin yawa ne suka je kantuna kuma sukan sayi wadannan litattafai.
A wani kantin sayar da litattafai na Beijing, Mr. Wang wanda ya yi aiki a wani kamfanin jarin waje da ke nan kasar Sin ya karanta wani littafin Zababbun Bayanai na Jiang Zemin har na tsawon mintoci 15. Lokacin da wakilinmu ya yi tattaunawa da shi, ya ce, har yanzu yana iya tunawa da wasu muhimman al'amuran da Mr. Jiang ya rubuta a cikin littafin. Zai iya ganin tarihin samun bunkasuwar kasar Sin daga wadannan litattafan Zababbun Bayanai na Jiang Zemin. "Ina tsammani, wadannan litattafai suna bayyana tunanin dukkan tsofaffin shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Tunanin da Mr. Jiang ya bayar a cikin litattafai ba nasa kawai ba, tunani ne na rukunin tsofaffin shugabannin kasar Sin. Suna bayyana tarihin yadda ake neman bunkasuwar kasar Sin. Za mu iya gane yadda suke mulki wata kasa."

Lokacin da Jiang Zemin yake rike da ragamar mulkin kasar Sin, tsarin raya tattalin arzikin kasuwanci na gurguzu ya yi ta samun cigaba a kai a kai. Kasar Sin ta kuma samu izinin shiga kungiyar cinikayya ta duniya, wato WTO. Sannan kuma, an dawo da yankin Hong Kong da yankin Macau a cikin duk kasar Sin. Kasar Sin ta kara bayar da gudummawarta sosai a duk duniya. Mutane da yawa wadanda suka karanta wasu bayanai sun bayyana cewa, suna jin dadin karanta su domin batutuwa da yawa da aka ambata a cikin bayanai sun shafi zaman rayuwarsu sosai. A ran 15 ga wata, a gun wani taro kan yadda za a yi koyi da Zababbun Bayanai na Jiang Zemin, Mr. Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin tsakiya na soja na kasar Sin na yanzu ya bayyana cewa, wadannan litattafan Zababbun Bayanai na Jiang Zemin suna da muhimmanci sosai ga halin da ake ciki yanzu a nan kasar Sin. "Yawancin ayyukan yadda ake neman bunkasuwa da abubuwan tarihi da aka ambata kuma aka yi nazari a cikin Zababbun Bayanai na Jiang Zemin muhimman abubuwa ne da muka taba shan juriyarsu da kanmu ko suka auku a wajenmu. Sannan kuma, abubuwan da aka ambata mun taba yinsu da kanmu, kuma za mu ci gaba da yinsu a nan gaba. Wasu tunani suna nan kusa da mu. Sabo da haka, muna jin dadin karanta su, kuma za mu samu tunani daga wadannan litattafai."
Kamar yadda yake kan mukamin kwayar sabon rukunin shugabannin kasar Sin, Hu Jintao ya yaba wa Jiang Zemin sosai wajen tunaninsa yin abubuwa domin jama'a. Mr. Hu ya kara da cewa, "Yadda za a iya yin nazari kan halin sauye-sauye da ake ciki a duk duniya daga duk fannoni bisa ilmin kimiyya, kuma yadda za a yi fama da kalubalen da duniyar da ke nufin ganiya masu yawa kuma ke raya tattalin arziki bai daya har kuma ke samun cigaban kimiyya da fasaha ta yi wa kasar Sin, kuma yadda za mu iya mallakar ikon neman bunkasuwar kasarmu. Sannan kuma, ta yadda za mu iya sanin ainihin halin matakin farko na gurguzu da kasar Sin ke ciki kuma yadda za mu iya ci gaba da bin manufar raya tattalin arziki da cimma burin wadata dukkan jama'ar kasar Sin. Dukkansu muhimman batutuwa ne da dole ne mu mai da hankali a kansu kuma da daidaita su a kai a kai yadda ya kamata." (Sanusi Chen)
|