Kwanan baya, mun sami wasika daga wajen mai sauraronmu Baba Zubair, mazauni garin Zaria na jhar Kaduna da ke Tarayyar Nijeriya. inda ya yi mana tambayoyi guda biyu, wato mene ne sirin da ke cikin fasahar warkarwa ta maganin gargajiya na Acupuncture. Sa'an nan, shin ko akwai dangantaka a tsakanin maganin gargajiya na kasar Sin da irin wanda ake amfani da shi a Afirka. A hakika, sabo da amfaninsa mai ban mamaki, har kullum maganin gargajiya na kasar Sin, musamman ma Acupuncture ya sami karbuwa sosai a Afirka da kuma duk duniya baki daya. A sa'i daya kuma, kullum jama'a suna sha'awar mene ne sirrinsa. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, bari mu tattauna fasahar Acupuncture ta kasar Sin da kuma hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka a fannin maganin gargajiya.
Acupuncture wata fasahar warkarwa ce ta musamman da ke cikin maganin gargajiya na kasar Sin. To, amma me ya sa ta ke iya warkar da mutane, mene ne sirrin wannan karamar allura kuma? Har zuwa yanzu dai, kimiyyar zamani ba ta iya bayyana dalilin sosai ba, sai dai kawai ra'ayin nan dangane da Jing da Luo a bakin Sinawa na samun karbuwa sosai. Ra'ayin yana ganin cewa, abin nan da ake kira Jing da Luo a bakin Sinawa, suna ko ina a cikin jikin mutum, kuma tamkar hanyoyi ne suke wadanda ke daukar kuzari da jini zuwa ko ina a jiki. Jing da Luo suna kuma hade da zuciya da dai sauran kayan jiki, sabo da haka, sun zama hanyoyin sadarwa na jikin mutum ke nan. Wadannan hanyoyin sadarwa kuma tamkar hanyoyi ban ruwa ne da ke cikin gona, wadanda ke jigilar kuzari da jini don gina jikin mutum. Ban da wannan, ana kuma ganin cewa, a jikin mutum, akwai wasu wurare na musamman wadanda tamkar mahada ne tsarin Jing da Luo, idan an sa allurai a wuraren, to, za a iya daidaita aikin tsarin nan na Jing da Luo, sa'an nan za a iya warkar da mutum.
Fasahar Acupuncture tana da tsawon tarihi. Amma ainihin allurar da aka yi amfani da ita a cikin fasahar, an yi ta ne da dutse.
Daga baya, bisa ci gaban fasahar narke karfe, sannu a hankali ne aka fara yin amfani da allurar da aka yi da karfe, kuma alluran karfe sun kara habaka fannonin da ake yin amfani da fasahar Acupuncture. Daga baya kuma, likitoci da yawa da suka kware a wajen fasahar Acupuncture sun fito, daga cikinsu akwai wani mai suna Huangfu Mi wanda ya rubuta cikakken bayani dangane da fasahar Acupuncture. Daga shekarar 256 zuwa 589 kuma, a zahiri dai aka kara samun bayanai dangane da fasahar Acupuncture, kuma a lokacin, fasahar Acupuncture ta yadu har zuwa kasashen Koriya da Japan da dai sauransu.
Ya zuwa lokacin daular Sui da Tang kuma, wato a tsakanin shekarar 581 zuwa 907, fasahar Acupuncture ta bunkasa har ma ta zama wani fannin nazari, kuma a hukumomin koyar da ilmin likita na lokacin, an kafa sashen musamman na koyon fasahar Acupuncture.
Bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekara ta 1949 kuma, fasahar Acupuncture ta sami bunkasuwa sosai. A halin yanzu dai, a cikin dukkannin asibitocin gargajiya sama da 2000 da ke barbazuwa a duk fadin kasar Sin, akwai sassan Acupuncture. A sa'i daya kuma, fasahar Acupuncture ta kuma yadu zuwa kasashe daban daban, ta zama makami mai karfi ne na dan Adam a wajen yaki da cututtuka iri iri.
Game da batun dangantakar da ke tsakanin maganin gargajiya na kasar Sin da na Afirka, to, kasashen Afirka suna da dogon tarihi na yin amfani da maganin gargajiya, a nata bangaren kuma, kasar Sin tana da cikakken tsari da kuma fasaha mai kyau a wajen yin maganin gargajiya nata. A sa'i daya kuma, bangarorin biyu suna kasancewa cikin hali mai kyau a wajen yin hadin gwiwa a fannin maganin gargajiya. Hadin gwiwar kuma tana shafar fannonin jiyya da ilmantarwa da nazari da ciniki da dai sauransu, kuma an cimma nasarori da dama. Tun daga shekara ta 1960, kasar Sin ta yi ta aikawa da kungiyoyin likitoci zuwa Afirka, don taimaka wajen kyautata halin da kasashen ke ciki a fannin kiwon lafiya da kuma horar da kwararru masu ilmin likitanci, da yada ilmin maganin gargajiya na kasar Sin, ta yadda za a kara fadakar da jama'ar kasashen Afirka dangane da maganin gargajiya na kasar Sin. Ban da wannan, jami'o'in ba da ilmin maganin gargajiya na kasar Sin suna kuma karbar dalibai daga kasashe da shiyyoyi masu yawa na Afirka, yanzu ana yin amfani da fasahar Acupuncture a kasashe da shiyyoyi da dama na Afirka. Bayan haka kuma, asibitoci da hukumomin nazari da jami'o'i da dai sauran sassan da abin ya shafa na kasar Sin suna kuma hada gwiwarsu tare da wasu kasashen Afirka a fannin maganin gargajiya. Don inganta hadin gwiwar da ke tsakaninta da kasashen Afirka kuma, a shekara ta 2002, kasar Sin da kungiyar kiwon lafiya ta duniya, wato WHO, sun kuma hada gwiwa sun shirya taron dandalin maganin gargajiya na Sin da Afirka a nan birnin Beijing. Maganin gargajiya na kasar Sin da maganin gargajiya na Afirka dukansu muhimmin kashi ne na nagartattun al'adun gargajiyar duniya. Muna imani da cewa, kara inganta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin maganin gargajiya, tabbas ne zai kawo alheri ga jama'ar bangarorin biyu, har ma ga 'yan Adam gaba daya. (Lubabatu)
|