Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-16 11:27:26    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(10/08-16/08)

cri
Ran 8 ga wata rana ce da ake bikin murnar sauran shekaru 2 da za a bude taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008 mai zuwa, a wannan rana, wani jami'in kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya bayyana cewa, ana gudanar da harkokin shirya taron wasannin Olympci na Beijing na shekarar 2008 yadda ya kamata a cikin shekarun nan biyar da suka wuce. Malam Wang Wei, mataimakin shugaban zartaswa kuma babban sakatare na kwamitin nan ya ce, shekarar 2006 da muke ciki shekara ce mai muhimmanci wajen aiwatar da shirye-shiryen da aka tsara don shirya taron wasannin Olympic na Beijing, sa'an nan kuma, za a gwada dukan ayyukan shiryawa a cikin shekara mai zuwa.

Mr. Wang Wei ya kara da cewa, yanzu yawan kwamitocin wasannin Olympic na kasashe da yankuna da suka yi shirin halartar taron wasannin Olympic na Beijing ya kai 203, wannan adadi ya kai 202 a gun taron wasannin Olympic na Athens. Wannan ya nuna cewa, mai yiwuwa ne taron wasannin Olympic na Beijing zai kasance taron wasannin Olympic ne da kasashe da yankuna za su fi halarta a cikin tarihi.

A wannan muhimmiyar rana kuma, shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa Mr. Jacques Rogge shi ma ya aika da wasika don taya murna.

Ran 10 ga wata, Mr. Liu Qi, shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya nanata wani batu da yawun gwamnatin kasar Sin cewa, gwamnatin kasar Sin za ta gatabar da sharuda masu sauki ga baki 'yan jarida a lokacin taron wasannin Olympic na Beijing bisa ka'idodin kasashen duniya suka saba da su.

Ran 8 ga watan Agusta, a nan Beijing, gidan rediyon kasar Sin ya fara watsa shirye-shirye kan wasannin Olympic cikin Sinanci da Turanci da Rashanci da Faransanci da Spaniyanci da Larabci da kuma Japananci da Jamusanci da harshen Korea har na tsawon awoyi 24 a hukunce, wanda gidan rediyo na farko da ke watsa shirye-shirye na musamman kan taron wasannin Olympic na Beijing da ayyukan shiryawa cikin wasu harsuna a kasar Sin har zuwa yanzu.

A cikin zagaye na karshen tsakanin mace da mace na budadiyyar gasar wasan kwallon tennis da aka kammala a ran 13 ga wata a Stockholm, bisa agogon wurin, 'yar wasan kasar Sin Zheng Jie ta lashe shahararriyar 'yar wasan kasar Rasha Anastasia Myskina da cin 2 ba ko daya, saboda haka ta sami lambar zinare ta uku a cikin gasa ta tsakanin mace da mace a duk rayuwarta ta wasan kwallon tennis.(Tasallah)