Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-16 11:22:22    
Yin hira da Yao Ming

cri

Dan wasan kasar Sin Yao Ming dan wasan kwallon kwando ne mafi shahara a kasar Sin, wanda ke aiki cikin kungiyar wasan kwallon kwando ta Houston Rockets ta NBA. Ya fara aikinsa a cikin gasar NBA tun daga shekarar 2002, yanzu ya zama daya daga cikin nagartattun 'yan wasan tsakiya na gasar NBA. Saboda lokacin hutu ya yi, Yao Ming ya dawo gida, don magance ciwon kafarsa, a sa'i daya kuma, ya share fage don wakiltar kasar Sin wajen shiga cikin gasar fid da gwani ta wasan kwallon kwando ta maza ta kasa da kasa da za a yi ba da dadewa ba. A kwanan baya, Yao Ming ya yi zantawa da wakilinmu, sun yi hira tare.

Lokacin da yake halartar wata harkar jin dadin jama'a da aka yi a kwanan baya, Yao Ming, wani tauraro ne da ke jawo hankulan mutane, ya yi zantawa da wakilinmu, ya kuma bayyana yadda yake ji a zuciyarsa ga masu kishin kwallon kwando da abokai na Internet. Game da yadda ya zama wani tauraro na wasan kwallon kwando, Yao Ming ya bayyana cewa,'lokacin da shekaruna ya kai 14, ina fatan sanya takalman wasa da aka kera da fata, a lokacin nan, na ji an ce, idan na shiga cikin kungiyar wasan kwallon kwando ta matasa ta kasar Sin, zan iya sanya irin wannan takalma, saboda haka, burina shi ne shiga cikin kungiyar matasa ta kasar, daga baya kuma, an ce, bayan shiga cikin kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin, zan iya biyan bukatata ta sanya takalma a ko wane lokaci, shi ya sa na yi kokarin shiga cikin kungiyar kasar Sin. Burina na da mai sauki ne, amma sun iya sa kaimi gare ni wajen yin kokarin samun horo da aiki, na sami ci gaba don cimma burina.'

Za a bude gasar fid da gwani ta wasan kwallon kwando ta maza ta kasa da kasa a kasar Japan a ran 19 ga wannan wata. Yao Ming dan wasa ne mafi muhimmanci ga kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin, shi ya sa a galibi dai makomar kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin a kasar Japan na dogaro da ko za a warkar da Yao Ming ko a'a. Game da raunin da ya ji, Yao Ming ya ce, an warkar da rauninsa da kashi 80 cikin dari. Za a bude wannan muhimmiyar gasa a ran 19 ga watan nan, wannan ya nuna cewa, ko da rauni ba zai ba Yao Ming matsala ba, amma lokacin yin horo tare da abokan kungiyar gare shi ya yi kadan sosai. Ko da yake haka ne, Yao Ming ya yi bayanin cewa, zai yi cudanya, zai yi ta yin mu'alama da 'yan kungiyar, don fahimtar juna. Ya kuma yarda da cewa, za a bukatci hakuri da lokaci wajen cimma burin fahimtar juna ta irin wannan hanya, amma ko kusa ba zai yi watsi da burin shiga cikin gasar fid da gwani ta wasan kwallon kwando ta duniya ba.

Ban da wannan kuma, an danka wa Yao Ming wani babban nauyi daban wato jagorancin kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin da ta sami maki mai kyau a cikin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Yao Ming ya ce,'makasudin da aka tsara a yanzu shi ne shiga cikin jerin nagartattun kungiyoyi 8, a sa'i daya kuma, ina fata za mu kara samun maki mai kyau, amma za mu bukaci kara yin kokari don cimma wannan buri, sa'an nan kuma, abubuwa masu yawa za su auku a cikin shekaru 2 masu zuwa, ba zan kiyasta abubuwan da za su faru ba, an matsa mini lamba sosai, ina fuskantar babban nauyi, kungiyarmu ta shiga cikin jerin nagartattun kungiyoyi 8 a gun taron wasannin Olympic na Athens, ko da yake mun sami wannan maki ne saboda kokarin da muka yi, amma mun taki sa'a a wasu fannoni. Dole ne mu nuna karfin zuciya a gun gasa.'

Saboda yana yin gasa a cikin gasar NBA a matsayin daya daga cikin wasu 'yan wasa na kasashen Asiya, shi ya sa Yao Ming ya fahimci gibin da ke tsakanin 'yan wasan kasashen Asiya, musamman ma 'yan wasan kasar Sin, da 'yan wasan nagartattun kungiyoyin kasa da kasa. Yana ganin cewa, gibi mafi girma da ke tsakanin nagartattun kungiyoyin kasashen Asiya, ga misali kungiyar kasar Sin da nagartattun kungiyoyin duniya shi ne karfin zuciya, ba karfin jiki ba ne. Ya ce,'a ganina, mun yi karancin karfin zuciya. Idan mun yi iyakacin kokarimmu wajen yin gasa tare da nuna karfin zuciya, ko mun kara da kungiyar Turai mafi karfi, ba za mu sha kaye daga hannunta da maki 10 ba. Mun yi karancin karfin zuciya. Mu kan fid da tsammani saboda maki 10, daga baya karfinmu ya ragu sannu sannu. Donme ba mu iya yin iyakancin kokarinmu a duk tsawon lokacin gasa na mintoci 40 ba, muna bukatar daidaita wannan matsala a fannin zuciya.'

Saboda abubuwan da ya fada, da sauki za mu iya gano cewa, a sakamakon yin gasa a cikin gasa ta koli har dogon lokaci, Yao Ming ya kyautata kansa sannu a hankali, yanzu ya riga ya kasance wani dan wasa mai kwazo, wanda ke da karfin zuciya, ya mayar da horo a gaban kome a fannin jin dadin rayuwarsa.(Tasallah)