Shekarar da muke ciki, shekara ce ta cika 50 da aka kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin sabuwar kasar Sin da kasashen Afrika. Tun wadannan shekaru 50 da suka shige, gudummowar da gwamnatin kasar Sin ta yarje wa kasashen Afrika ta taka muhimmiyar rawa ga kasashen da abun ya shafa a fannin ingiza bunkasuwar tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da kuma daga matsayin ilmantarwa da aikin jiyya da kiwon lafiya da dai sauran fannoni.
Sanin kowa ne, tun bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin, ta yarje wa kasashen Afrika gudummowa a fannoni da dama ba tare da kowane sharadi ba, wadda ta samu babban yabo daga gwamnatocin kasashe da jama'a na Afrika. Yin haka, ya taka muhimmiyar rawa ga kasar Sin da kasashen Afrika wadanda suka zama dauwamammun aminai da sahihan abokai da kuma 'yan-uwa masu raba fara daya.
Jama'a masu sauraro, kuna sane da, cewa tun daga karshen shekarar 1963 zuwa farkon shekarar 1964, marigayi firaminista Zhou Enlai na kasar Sin ya kai ziyarar aiki ta sada zumunta a kasashe 10 na Afrika, inda ya gabatar da ka'idoji 8 kan gudummowar da kasar Sin take yarje wa kasashen ketare a fannin tattalin arziki da fasaha. Marigayi Zhou En-lai ya jaddada, cewa gwamnatin kasar Sin ta girmama mulkin kan kasashe masu karbar gudummowa sosai, kuma ta ba da gudummowa ne ba tare da kowane sharadi ba. Kawo yanzu, wannan ka'ida ta zama muhimmiyar manufa dake bada jagoranci ga gwamnatin kasar Sin wajen yarje wa kasashen Afrika gudummowa.
Daga shekarar 1950 zuwa shekarar 1969, muhimmin salon da gwamnatin kasar Sin take bi wajen yarje wa kasashen Afrika gudummowa, shi ne gina manyan ayyuka, da samar da kayayyaki da kuma aikewa da kwararru da masana. Amma tun daga shekarar 1978 bayan da aka soma aiwatar da manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen ketare a kasar Sin ; A nasu bangaren, kasashen Afrika su ma sun soma yin kwaskwarimar tsarin tattalin arziki. To bisa wannan sabon hali dai, bangarorin biyu wato Sin da kasashen Afrika dukansu sun kara mai da hankali kan yadda za a samu babbar moriya a fannin tattallin arziki daga gudummowa da kuma rawar da gudummowar za ta taka wajen kara yin musanye-musanye tsakanin bangarorin biyu a fannin tattallin arziki da cinikayya. Wato ke nan, an raba masu bada gudummowa da masu aiwatar da ayyukan gudummowa sannu a hankali. Sakamakon haka, wassu kamfanoni da masana'antu masu karfi wadanda kuma suke da kwarjini a zukatan jama'a sun taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da ayyukan gudummowa. Abun da ya fi jawo hankulan jama'a, shi ne tun daga shekarar 1990, gwamnatin kasar Sin ta sanya matukar karfi lokacin da take yarje wa kasashen Afrika gudummowa a fannin kulawa da ba da jagoranci a fannin fasaha, da ba da rancen kudi tare da nuna kyakkyawan gatanci, da zuba jari a fannin cinikayya, da ragewa da kuma cire basussukan da kasashe mafi talauci suka ci ,da horar da jami'an tattalin arziki da cinikayya da kuma na bada taimakon agaji cikin gaggawa a sanadiyyar aukuwar bala'in da Allah ya saukar da dai sauran fannoni.
Aminai masu sauraro, idan an kwatanta da gudummowar wassu kasashen yamma, to ana ganin, cewa sigar musamman mafi girma ta gudummowar da kasar Sin take yarje wa kasashen Afrika ita ce sahihiya ce kuma maras son kai ,wato ke nan ba ta bidar kowace irin moriya ba kuma ba ta taba matsa lamba ga kasashen Afrrika ba, balle yin kane-kane ga harkokin gida da na waje na kashen Afrika. Ban da wannan kuma, wani irin muhimmin salon da gwamnatin take bi wajen yarje wa kasashen Afrika gudummowa, shi ne ta hanyar da ba ta kudi ba wato ba kamar yadda wassu kasashen Yamma suke yi ba. Hakikanan abubuwa sun shaida, cewa irin wannan salon da kasar Sin take bi wajen bada gudummowa ta hanyar samar da kayayyaki da kwararru da masana ya fi share hawayen kasashe masu karbar gudummowa da kuma kara kyautata huldar dake tsakanin bangarorin biyu a fannin tattalin arziki da cinikayya. Tun a shekarar 2003, shugabannin gwamnatocin kasashen Afrika kamar su Madagascar, da Eriteria da kuma Rwanda da dai sauransu sun nuna godiya da yabo ga gwamnatin kasar Sin bisa gudummowar da ta yarje musu yayin da suke nuna rashin jin dadi ga wassu kasashen yamma saboda sukan yarje musu gudummowa ne tare da sharadi maras daidaici; Wassu shugabannin kasashen Afrika har sun yi kira ga yin watsi da irin wannan gudummowa.
Ana farin ciki da ganin, cewa gudummowar da gwamnatin kasar Sin ta yarje wa kasashen Afrika ba ma kawai ta kara kyautata dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a fannin tattalin arziki da cinikayya ba, har ma ta daukaka ci gaban amincewa da juna tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a fannin siyasa da kuma ingiza musanye-musanyen da sukan yi a fannin diplomasiyya. ( Sani Wang )
|