Yau wato ran 15 ga wata, firayim minista Koizumi Junichiro na Japan ya sake kai ziyarar ban girma ga makabartar Yasukuni, inda ake bauta wa manyan masu laifufukan yaki na babban yakin duniya na 2. Gwamnatin kasar Sin ta kai kara da babbar murya ga wannan danyen aikin da aka yi wanda ya bakanta ran jama'ar kasashen da suka sha barnar yakin kai hari da masu ra'ayin nuna karfi na Japan suka tayar, da tauye harsashen siyasa na dangantakar da ke tsakanin Sin da Japan. To, ga cikakken bayanin game da wannan labari.
A ran 15 ga watan Agusta na kafin shekaru 61 da suka wuce,, kasar Japan ta sanar da cewa ta ci hasarar yaki kuma ta ba da kai ba tare da wani sharadi ba, jama'ar Sin da na sauran kasashen Asiya sun ci nasarar kin yakin kai hari da Japan ta tayar. Liu Jianchao, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana cewa,
"Kasar Sin kasar ce wadda sha barna mafi tsanani daga wajen yakin kai hari da masu ra'ayin nuna karfi na Japan suka tayar kan kasashen waje, jama'ar Sin kuma sun sha wahaloli masu tsanani daga wannan yaki. Firayim minista Koizumi Junichiro ya yi ta bakanta ran jama'ar Sin kan matsalolin tarihi, sabo da haka ba ma kawai ya ci amanar kasashen duniya ba, hatta ma zai ci amanar jama'ar Japan, kuma ya tauye suna da moriya na kasar Japan."
Tun daga watan Afrilu na shekarar 2001 na bayan da Koizumi Junichiro ya zama firayim ministan Japan, yakan kai ziyarar ban girma ga makabartar Yasukuni a kowace shekara, sabo da haka dangantakar da ke tsakanin Sin da Japan ta fada cikin mawuyacin hali. A ran 31 ga watan Maris na wannan shekara a nan birnin Beijing, yayin da Hu Jintao, shugaban kasar Sin ke ganawa da shugabannin kungiyoyi 7 masu sada zumunci tsakanin Japan da Sin ya bayyana a fili cewa, muhimmin dalilin da ya sa dangantakar da ke tsakanin Sin da Japan ta samu wahala shi ne, sabo da tsirarun shugabannin kasar Jpan sun tsaya ga kai ziyarar ban girma ga makabartar Yasukuni, inda ake bauta wa manyan masu laifufukan yaki na babban yakin duniya na 2, wannan ya bakanta ran jama'ar kasashe masu shan wahalolin yaki ciki har da jama'ar kasar Sin, kuma ya tauye harsashin siyasa na dangantakar da ke tsakanin Sin da Japan. Farfesa Gao Hong, direktan ofishin binciken siyasa na hukumar binciken kasar Japan ta cibiyar binciken kimiyyar zaman al'ummar Sin ya bayyana cewa, wannan ya zama wani babban mugun aiki ne da Koizumi Junichiro ya yi cikin zaman rayuwarsa na fannin siyasa.
"Lalle Koizumi Junichiro ya nuna taurin kai tana barkata mugunta ba tare da nuna damuwa ga sakamakon da zai samu ba. Daga wani fanni ya tada tsokana ga kasar Sin da ta Korea ta Kudu ta hanyar yin danyen aikin kai ziyarar ban girma ga makabartar Yasukuni bisa matsayinsa na firayim ministan majalisar ministoci, daga wani fanni daban wato fannin harkokin kasar Japan kuma, ya yi biris da ra'ayoyin jama'ar Japan da kiyayyar da sassa daban-daban na zaman al'umma ke yi masa domin tafiyar da manufar siyasa ta kansa. Wannan wasan karshe ne da ya yi, amma mugun wasa ne sosai."
Mr. Liu shi ma ya bayyana cewa, "Gwamnatin Sin da jama'arta za su hada kansu tare da dukkan 'yan siyasa da kuma jama'a na kasar Japan wadanda ke girmama da dukufa kan sada zumunci tsakanin Sin da Japan, bisa harsashin takardun siyasa guda 3 tsakanin kasashen 2, za su tsaya ga yin zama tare cikin lumana da samun bunkasuwa tare."
|