Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-15 16:53:09    
Birnin Yining

cri

A wannan mako ma za mu kawo muku shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin wanda mu kan gabatar muku a ko wane mako. A cikin shirinmu na yau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan birnin Yining, babban birni ne na Yili na jihar Xinjiang ta kasar Sin, daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayani, inda za mu gabatar muku da wani iri shahararren abinci na kasar Sin, wato gasasshiyar agwagwa ta Beijing.(music)

Birnin Yining yana da dogon tarihi, inda 'yan kabilu da yawa suke zama, haka kuma ana iya fahimtar al'adu iri daban daban, shi ya sa birnin Yining yake da hali na musammam. Yining yana da muhimmanci sosai wajen zirga-zirga tsakanin kasashen gabas da yamma, tun daga shekarar 206 kafin haihuwar Annabi Isa har zuwa shekarar 220 Yining ya kasance babban birni ne wajen ciniki a kan hanyar siliki ta arewa ta gargajiya a kasar Sin, wanda ya hada kasashen Asiya ta Tsakiya da ta Yamma da kuma kasashen Asiya ta Kudu da wurare daban daban na Turai.

Tsohon wurin tarihi na gidan ibada na Jinding yana gabashin wannan birni, wanda Lama suka kafa a farkon karni na 18, ya yi suna ne sosai. Dalilin da ya sa ake kiran shi Jinding shi ne saboda rufinsa na zinare, ma'anar Jin a Sinanci ita ce zinare, ma'anar Ding ita ce rufi. An rushe shi a cikin yake-yake a shekarar 1775.

Kogon dutse mai suna Huolong yana tudu na yamma da ke kwarin Tiechang na kauyen Bayandai na arewa maso yammacin birnin Yining. Saboda kwal da ke gindin tudu ya kunna da kansa, shi ya sa iska mai amfani a jiki tana fitowa daga karkashin kasa, yana iya magance wasu ciwace-ciwacen da aka dade ba a iya warkar da su ba, saboda haka, mutane sun haka ramuka a inda iskar ke fitowa don magance ciwace-ciwace.

Kogin Yili yana gudu a kudancin birnin Yining, an gina babbar gadar kogin Yili a tsohuwar tashar jiragen ruwa ta kogin Yili a shekarar 1975.

A kofa ta kudu ta birnin Yining, ya kasance da masallaci na Baitula, wanda masallaci ne mafi tsufa na kabilar Uygur a birnin Yili, fadinsa ya kai muraba'in kadada 18.

Yanayi yana da kyau a nan Yining, an dasa bishiyoyin tuffa wato apple trees a gefen hanyoyi, shi ya sa ana kiran Yining birnin Apple. An samu dajin bishiyoyi masu ba da 'ya'ya na asali a Yining, wanda ba a taba samunsa a duk fadin kasar Sin ba, kwararru da yawa suna ganin cewa, mai yiwuwa ne birnin Yining yana daya daga cikin wuwaren da aka dasa bishiyoyin tuffa a duk duniya.

To, jama'a masu sauraro. Muna muku godiya da saurarenmu, kuma muna fatan za ku ci gaba da sauraren shirin nan na yawon shakatawa a kasar Sin.