Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-15 16:51:21    
Gasasshiyar agwagwa ta Beijing

cri

Mutanen da suka kawo wa Beijing ziyara su kan ji cewa, mutumin da bai je babbar ganuwar kasar Sin ba shi ba namiji ba ne, haka kuma, dukan wadanda ba su ci gasasshiyar agwagwa ba su kan yi da na sani. Wannan gaskiya ne, idan wani ya kawo wa Beijing ziyara, bayan da ya ziyarci shahararriyar babbar ganuwa ta kasar Sin, bai ci gasasshiyar agwagwa ta Beijing ba, zai yi da na sani. A cikin shirin da za su ci gaba da karanta muku, za mu dan gutsura muku da wannan gasasshiyar agwagwa ta Beijing.

Gasasshiyar agwagwa ta Beijing ya fito a nan Beijing yau da shekaru dari 7 da suka wuce. An gasa agwagi ta hanyoyi 2, hanya ta farko ita ce, yin amfani da itace a cikin murhu, daga baya an rataya agwagi kan wuta, sai a gasa su kai tsaye. Wata hanya daban ita ce, a maimakon gasa agwagi a kan wuta kai tsaye, a kan yi amfani da zafin bangon murhu wajen gasa agwagi, saboda zafin murhu ya ragu sannu sannu, shi ya sa yayin da ake cin gasasshiyar agwagwa, fatarta na garas-garas, tana da dadin ci sosai.

Dakin cin abinci mai suna 'Bian Yi Fang' dakin cin abinci ne mafi tsufa da ya shirya gasasshiyar agwagwa ta Beijing a nan Beijing, wanda shekarunsa ya kai misalin dari 6. Yanzu, dakin cin abinci na Bian Yi Fang ya kafa ressansa da dama a Beijing, babban zaurensa yana kusa da mahadar hanya ta Chong Wen Men mai ni'ima da ke cibiyar Beijing. Da zarar ka shiga cikin wannan babban zaure, sai ka fahimci halin musamman na al'adun kasashen Gabas sosai. Dukan kayayyakin da ke cikin wannan babban zaure sun nuna halin musamman na al'adun gargajiya na kasar Sin.

Manaja na wannan babban zaure Mr. Song Yan ya bayyana cewa, halin musamman mafi girma da dakin cin abinci na Bian Yi Fang yake da shi shi ne yin amfani da zafin bangon murhu wajen gasa agwagi a maimakon gasa su kan wuta kai tsaye. Ya ce,(murya ta 1, Song Yan)

'mun yi amfani da zafin bangon murhu wajen gasa agwagi a maimakon gasa su kan wuta kai tsaye, agwagi za su nuna saboda raguwar zafin bangon murhu. Fasahar wannan hanya ta fi ta hanyar gasa agwagi kan wuta kai tsaye wuya kadan. Agwagin da muka shirya ba ma kawai fatansu na garas-garas ba yayin da ake ci, har ma namansu na da dadin ci, launin fatarsu na da kyau.'

Ban da dakin cin abinci na Bian Yi Fang kuma, dakin gasa agwagi mai suna Quan Ju De wani dakin cin abici ne daban da ke shirya gasasshiyar agwagi mai dadin ci a Beijing. Yanzu Dakin gasa agwagi na Quan Ju De ya kafa ressansa a wurare daban daban a duniya, yau ma za mu gabatar muku da wani reshen dakin gasa agwagi nasa a Qian Men a nan Beijing. Shekarun wannan dakin gasa agwagi ya kai fiye da dari 1, wanda ba ma kawai wuri ne da aka ci gasasshiyar agwagwa ba, har ma shahararren wurin shakatawa ne. An yi ado ga bene na farko na wannan dakin gasa agwagi kamar yadda yake a cikin shekaru 30 na karnin jiya.

Kukun dakin gasa agwagi na Quan Ju De sun gasa agwagi kan wuta kai tsaye a cikin murhu. Kafin suka gasa su, sun shafa miyar musamman tasu a kan fatan agwagi, sa'an nan kuma, lokacin gasa agwagi, sun shirya wuta yadda ya kamata, a sakamakon haka, jan fatan gasassun agwagi ya yi kama da na dabino, suna da dadin ci kwarai.

Dalilin da ya sa gasassun agwagi da dakin gasa agwagi na Quan Ju De ya shirya suke jawo hankulan mutane shi ne saboda yana da nasaba da hanyoyin da ake bi wajen fere agwagi da cinsu. Manaja na reshen dakin gasa agwagi na Qian Men Mr. Ma Zhe ya yi bayanin cewa,(murya ta 2, Ma Zhe)

'a galibi dai kuku sun fere neman wata gasasshiyar agwagwa har yanka 108 a cikin ko wane faranti. Daga baya, masu cin abinci su kan ci wadannan gasasshiyar agwagwa tare da miyar musamman ta kasar Sin wato Tian Mian Jiang a bakin Sinawa, don rage man da ke cikin naman agwagwa.'

Ba ma kawai Sinawa suna son cin gasasshiyar agwagwa ta Beijing ba, har ma mutanen kasashen waje da yawa suna son cin irin wannan gasasshiyar agwagwa. A cikin dakunan gasa agwagi manya da kanana na Beijing, ko kusa a ko wace rana mutanen kasashen waje sun zo Beijing don cin gasasshiyar agwagwa. Mr. Peter Kuttel, dan kasar Switzerland, ya darajanta gasasshiyar agwagwa ta Beijing sosai. Ya ce,(murya ta 3 Mr. Kuttel)

'ina jin cewar gasasshiyar agwagwa na da dadin ci kwarai, sa'an nan kuma, ina mamaki sosai saboda an yi ayyuka da yawa wajen gasa agwagi. A cikin dakin cin abinci, na ga yadda ake gasa agwagi a ckiin murhu, haka kuma, na ga an ci wannan gasasshiyar agwagwa tare da wasu sauran abubuwa. A takaice dai, gasasshiyar agwagwa ta Beijing tana da dadin ci, kuma tana da dadin musamman, ina sha'awar cinta sosai.'