Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-15 16:35:01    
Jama'ar Sin da kasashen Afirka suna kara sada zumunci ga juna

cri

Sha'anin sada zumunci da ke tsakanin jama'ar Sin da kasashen Afirka ya zama wani sashe mai muhimmanci na manyan manufofin diplomasiyya da kasar Sin take gudanar. A shekarar 1960, an kafa hadaddiyar kungiyar sada zumunci da ke tsakanin jama'ar kasar Sin da kasashen Afirka ta kasar Sin. Daga lokacin, kungiyar ta yi aiki da yawa kuma ta sami nasarori sosai wajen sada zumunci da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da kara sa kaimi wajen gama kai a kan tattalin arziki da cinikayya da suka yi da kara yin cudanyar al'adu da tsakanin bangarorin biyu.

Hadaddiyar kungiyar sada zumunci da ke tsakanin jama'ar kasar Sin da kasashen Afirka ta kasar Sin tana aiki bisa tushen kara samun kawaye a duk fannoni. Kungiyoyin sada zumunci da ke tsakanin Sin da Afirka a Afirka suna kasancewa manyan kawaye a Afirka. Mutane da ke abokantaka da kasar Sin a Afirka su kan kafa irin wadannan kungiyoyi, kuma sun bayar da muhimmiyar guddummuwa wajen bayyana ra'ayin kasar Sin da zurfafa aminci da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka. Hadaddiyar kungiyar sada zumunci da ke tsakanin jama'ar kasar Sin da Afirka ta kasar Sin ta kaddamar da kyautar manzon sada zumunci da ke tsakanin Sin da Afirka domin nuna yabo da godiya ga wadanda suke ba da taimako ga sha'anin sada zumunci da ke tsakanin Sin da Afirka. Shugaban kungiyar ada zumunci da ke tsakanin jama'ar kasar Sin da Madagascar ya taba samun wannan kyauta.

Hadaddiyar kungiyar sada zumunci da ke tsakanin jama'ar kasar Sin da Afirka ta kasar Sin tana mai da hankali sosai a kan samun kawaye a rukunoni daban daban na kasashen Afirka, musamman manyan mutane a Afirka. A cikin shekaru fiye da 20 da kasar Sin take gudanar da manufar bude kofa ga duniya da yin gyare gyare a gida, kungiyar ta riga ta gayyaci manyan mutanen Afirka da yawa domin su kai ziyara a kasar Sin, wadanda suka hada da tsohon shugaban kasar Seychelles da mataimakin shugaban majalisar dokoki na kasar Kodivwa da ministan raya kasa na kasar Habasha da ministan harkokin gida na kasar Djibouti da ministan harkokin shugaban kasa na Saliyo da dai sauransu. To, ta wadannan ziyarce ziyarce da suka kai a kasar Sin, sun kara sanin kasar Sin kuma sun kara sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka.

A watan Janairu na shekarar 2003, ministan harkokin shugaban kasa na Uganda ya kai ziyara a kasar Sin bisa gayyatar da adaddiyar kungiyar sada zumunci da ke tsakanin jama'ar kasar Sin da Afirka ta kasar Sin ta yi masa. Da ya koma kasar Uganda, kai tsaye ne ya je ofishin jakadanci na kasar Sin da ke Uganda domin halartar bikin bazara da aka shirya. A gun bikin, minista ya nuna yabo a kan nasarorin da kasar Sin ta samu wajen bunkasa tattalin arziki, kuma ya sanya ran alheri ga makomar gama kai da ke tsakanin kasashen biyu, ya bayyana wa dukkan Sinawa a wurin cewa, 'Idan kuna da ko wane abu a nan gaba, sai ku je wurina kai tsaye, mu 'yan uwa ne, ni wani basinne mai bakar fata.' Bayan da minista ya zama mataimakin shugaban kasar Uganda, ya ci gaba da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

To, hadaddiyar kungiyar sada zumunci da ke tsakanin jama'ar kasar Sin da Afirka ta kasar Sin da sauran kungiyoyin jama'a na Sin da na kasashen Afirka da sauran mutane sun yi kokari sosai domin kara sada zumunci da tsakaninsu. Sabo da haka, mun yi imani cewa, dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka tana da wata kyakkyawar makoma.(Danladi)