Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-14 15:06:46    
Kabilar Bai

cri

Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kananan kabilun kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu gabatar muku da bayani kan kabilar Bai ta kasar Sin, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani a karkashin lakabi haka: Kasar Sin ta karfafa kare al'adun gargajiya na kananan kabilun kasar. To, yanzu ga bayani.

Kabilar Bai tana cikin kudu maso yammacin kasar Sin, kuma ita wata karamar kabila ce mai dogon tarihi da al'adun gargajiya. An fi samun 'yan kabilar a shiyyar Dali na kabilar Bai mai cin gahin kai da biranen Lijiang da Kunming da sauransu da ke jihar Yunnan ta kasar Sin. Bisa kidayar yawan mutanen kasar Sin ta karo na biyar da aka yi a cikin shekara ta 2000, yawan 'yan kabilar Bai ya kai fiye da miliyan 1.8. 'Yan kabilar suna yin amfani da harshensu, wato harshen Bai, amma ba su da harafi, suna yin amfani da harafin kabilar Han.

Bayan kafuwar kasar Sin, a karkashin shugabancin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, daya bayan daya ne, 'yan kabilar Bai sun kammala yin gyare-gyare na demokuradiyya da na gurguzu. A watan Nuwamba na shekara ta 1956, an kafa shiyyar Dali ta kabilar Bai mai cin gashin kai.

A cikin shekaru fiye da 50 da aka kafa Jamhuriyyar Jama'ar Kasa Sin, musamman ma bayan taro na uku na dukkan wakilai na kwamitin tsakiya na 11 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka yi a cikin shekara ta 1978, shiyyar Dali ya samu babban ci gaba wajen sha'anonin masana'antu da noma. Bugu da kari kuma, sha'anonin ilmi da kiwon lafiya sun samu bunkasuwa sosai. Ana iya samun furfesa da marubuta da likitoci da kwararrun kimiyya da fasaha da yawa na kabilar Bai. An riga an warkar da ciwon tsotsar jini da aka taba yaduwa sosai kafin kafuwar kasar Sin. Yanzu zaman 'yan kabilar Bai ya samu kyautatuwa kwarai da gaske.

'Yan kabilar Bai suna bin addinin Buddhism. "Titin Maris" wata babbar salla ce ta kabilar. A ko wace shekara, daga ran 15 zuwa ran 20 na watan Maris bisa kalandar gargajiyar ta kasa Sin, an yi sallar a gindin dutsun Diancang da ke yammacin birnin Dali. Da farko sallar wata salla ce ta addinin Buddhism, daga baya kuma sannu a hankali a kan yin cinikayya a cikin sallar. Bayan kafuwar jamhuriyyar jama'ar kasar Sin, sallar "titin Maris" ta riga ta zama babban taron yin cudanyar kayayyaki da kuma wasannin motsa jiki na kananan kabilu da a kan yi a ko wace shekara.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, kasar Sin ta karfafa kare al'adun gargajiya na kananan kabilun kasar.