Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-14 15:17:40    
Mutane masu yawa suna koyon Sinanci a duk duniya

cri

Har kullum a kan zabi Turanci idan ana son koyon harshe na biyu, haka ne, ya zuwa yanzu Turanci wani muhimmin harshe ne a duk duniya. Amma sabo da bunkasuwar tattalin arziki na kasar Sin, mutane masu yawa sun zabi Sinanci da ya zama harshe na biyu. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yanzu mutane fiye da miliyan 30 wadanda harshe na farko ba Sinanci ba suna koyon Sinanci, kuma wasu daga cikinsu suna ganin cewa, kwarewa wajen iya magana da Sinanci ya zama wani muhimmin abu ne idan wani mutum ko wani kamfani yana so ya sami fifiko tsakanin takarar da ake yi.

Kerstin Storm wata daliba ce ta jami'ar Minstel ta kasar Jamus. Lokacin da take makarantar sakandare, ta yi sha'awar ga Sinanci da kuma kasar Sin sosai. Amma a wancan lokaci, ba a koyar da Sinanci a cikin makarantar sakandare da take ciki ba, shi ya sa ba ta iya cimma burinta ba. Lokacin da ta shiga jami'a, Kerstin ta zabi koyon Sinanci. Bayan da ta yi karatu cikin shekaru 4, yanzu ta riga ta iya yin amfani da Sinanci wajen yin hira tare da abokanta Sinawa. Ta gaya wa wakilinmu cewa, koyon Sinanci yana da kyau sosai.

"yanzu muna da dama da yawa wajen neman samun aikin yi a cikin kasar Sin, sabo da akwai kamfanonin Jamus masu yawa a Sin, kuma ana ta karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen Jamus da Sin a fannin kasuwanci. Shi ya sa a ganina, koyon Sinanci zai ba ni taimako wajen neman samun aikin yi. "

A hakika dai, Sinanci wani irin harshe ne da ba za a iya sarrafa shi da sauki ba, masu koyon Sinanci musamman ma na kasashen yamma su kan sha wahala sosai wajen lafazi da harafi na Sinanci. Amma sabo da kasar Sin tana kara bude kofa ga kasashen waje, tattalin arzikinta yana ta samun karuwa cikin sauri, kuma kasar Sin tana karfafa yin cudanya tsakaninta da kasashen duniya, shi ya sa mutanen waje mafi yawa suna kaunar koyon Sinanci.

Bugu da kari kuma gwamnatocin kasashe masu yawa sun fara mai da hankulansu kan ayyukan koyar da Sinanci. Jami'in ma'aikatar ilmi ta kasar Vietnam Vu Minh Tuan ya bayyana cewa, "yanzu daliban kasar Vietnam suna son koyon Sinanci kwarai da gaske. Ban da jami'o'in Vietnam, akwai cibiyoyi da yawa wajen koyar da Sinanci, dalibai da dimbin yawa su kan koyi Sinanci a lokacin hutu."

Domin jarraba Sinanci da mutanen kasashen waje suke iyawa, tun shekara ta 1991, kasar Sin ta shirya wata jarrabawa, wadda ake kiranta HSK. Ya zuwa yanzu, akwai tashoshin jarrabarar HSK fiye da 150 a cikin kasashen 34, ta yadda masu koyon Sinanci na kasashe daban daban za su iya shiga jarrabawar da sauki. An ce, bayan da suka samu takardun shaidar matsayin Sinanci da abin ya shafa, mutanen kasashen waje sun iya neman shiga kwalejoji da jami'o'i iri daban daban na kasar Sin.

Mu Xiaolong, wani dan kasar Amurka, ya shiga jarrabawar HSK sabo da dalilin da aka ambata a baya, ya ce "dalilan da suka sa na shiga jarrabawar HSK su ne, da farko, ina fatan zan gano matsayina a fannin Sinanci, da kuma abubuwan da nake bukatar in kyautata su. Na biyu, jarrabawar HSK jarrabawa ce da gwamnatin kasar Sin ta shirya,idan ina son in yi karatu in sami digiri na biyu a kasar Sin, to ana bukatar takardar shaidar matsayin Sinanci na 6."

A cikin shekarun nan da suka gabata, mutane masu yawa suna koyon Sinanci a duk duniya, shi ya sa matsalar karancin Malamai masu koyar da Sinanci ta kara tsanani. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin ta tsai da shawarar kafa kwalejojin Confucius a kasashen waje ta hanyar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen waje, ta yadda mutanen waje za su iya koyon Sinanci da kuma fahimtar al'adun gargajiya na kasar Sin. Ya zuwa yanzu, an riga an kafa kwalejojin Confucius 80 a cikin kasashe da shiyyoyi 36.

Kasar Sin za ta ci gaba da aika da masu sa kai zuwa kasashe daban daban a nan gaba domin koyar da Sinanci da kuma ba da taimako ga ma'aikatun ilmi na kasashen nan wajen ayyukan koyar da Sinanci. A waje daya kuma, hukumomin kasar Sin da abin ya shafa za su karfafa kyautata sharudda da kayayyakin koyar da Sinanci na kasar Sin domin samar da ayyukan hidima mafi kyau ga dalibai masu dalibta na kasashen waje. Kande Gao)