Ran 11 ga wata, a Geneva, kwamitin hakkin Bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya shirya taron musamman kan halin da kasar Lebanon ke ciki. A cikin jawabin da ya yi, zaunannen wakilin kasar Sin da ke hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da ke Geneva Mr. Sha Zukang ya bayyana cewa, bangaren kasar Sin ya ki yarda da dukan matakan da za su lalata kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya, ya kuma yi kira ga bangarori daban daban masu gwagwarmaya da juna na kasashen Lebanon da Isra'ila da su daina yin gaba da juna nan da nan.
Ban da wannan kuma, Mr. Sha ya yi kira ga bangarori masu gwagwarmaya da juna da su yi iyakacin kokarinsu su yi hakuri, don magance jin wa fararen hula rauni da kuma lalacewar halin da ake ciki.
A cikin jawabin da ta yi, babbar jami'ar musamman ta kwamitin hakkin Bil Adama madam Louise Arbour ta bukaci a yi bincike kan halin da ake ciki wajen taka hakkin Bil Adama a cikin rikicin da ke tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila, ta kuma yi gargadin cewa, mai yiwuwa ne za a yanke hukunci ga mutanen da ake tuhumarsu da laiffuffukan yake-yake ko kuma yin adawa da dan Adam.(Tasallah)
|