Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-10 17:47:45    
Kasar Sin za ta kara ware kudade don ba da goyon baya ga raya aikin ba da hidimar kiwon lafiya a unguwoyin birane

cri
A ran 10 ga wannan wata a nan birnin Beijing, wani jami'in ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara ware kudade da dauki sauran matakai don ba da goyon baya ga raya ayyukan kiwon lafiya a unguwonin da ke birane don daidaita wahalolin da jama'a suke sha wajen shawo kan ciwace-ciwacen da suke kamuwa tare da biyan kudadde da yawa.

Malama Hao Jia tana zama a yankin Shijingshan na birnin Beijing, lokacin ba ta da lafiya, sai ta je ganin likita a asibitin Shijingshan da ke nesa da gidanta da kilomita uku. Kwanan baya ta ji rauni bisa sakamakon cizon da karamin karenta ya yi mata, sai nan da nan ta tafi zuwa wata ciniyar ba da  kiwon lafiya da ke unguwar da take zama ba tamkar yadda ta kan je zuwa asibitin Shijinshan ba, ashe tana ganin cewa, ta sami sauki wajen warkar da ciwo a tashar nan. Ta bayyana cewa, a cibiyar nan, ba a sami marasa lafiya da yawa ba, likitoci suna son karbar mutane sosai, sun tambaye ni dalilin da ya sa zuwana a can, sai na gaya musu cewa, karena ne ya cije ni, ina son a sa mini allurar yin rigakarin maganin cizon mahaukacin kare, sai nan da nan sun sa mini allurar, kai minti daya ko biyu ke nan. A da na kan tafi asibitin Shijingshan, amma dole ne na kashe lokuta da yawa , kuma na gaji sosai a kan hanya.

A da, dayake manyan albarkatan kiwon lafiya na biranen kasar Sin suna cunkushewa a manyan asibitoci, mutanen kasar Sin da yawa sun saba da dudduba likitoci a manyan asibitoci ko ciwacen-ciwacen da suke kamuwa masu tsanani ne ko marasa tsanani. Amma bayan shekaru 90 na karnin da ya wuce, kasar Sin ta soma kafa cibiyoyin ba da hidimar kiwon lafiya a unguwoyi don samar da hidimar kiwon lafiya ga mutanen da suke zama a unguwoyin birane, wannan ya kawo sauki ga mutanen da suke je dudduba lafiyarsu a wuraren da ke kusa da gidajensu, sa'anan kuma gwamnati ta bayar da matakai da yawa don ba da taimako ga ingiza ayyukan nan, kuma a kai a kai ne aka kafa tsarin ba da hidimar kiwon lafiya a unguwoyin birane.

Yanzu, mutane suna ganin cewa, an kafa wadannan tashoshin ba da hidimar kiwon lafiya a wuraren da ke dab da gidajensu , sun iya sauka tashoshin nan da minti 15 kawai ta hanyar tafiya da kafa kawai, kuma kudin arha ne da suka kashe domin samun magunguna.

Mataimakin ministan ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin Jiang Zuojun ya bayyana cewa,a nan gaba, kasar Sin za ta kara ware kudade don ba da goyon baya ga raya ayyukan kiwon lafiya a unguwoyin birane, ya bayyana cewa, gwamnati ta ware kudade don ba da karin kudin taimako ga hukumomin ba da hidimar kiwon lafiya na unguwoyin birane wajen gina manyan ayyuka da gyara gidaje da sayen manyan na'urori da horar da mutane da ba da hidima wajen kiwon lafiyar jama'a da kudaden da aka kashe domin wadanda suka yi ritaya.

Mr Jiang Zuojun ya bayyana cewa, gwamnati ita ma ta maraba da kungiyoyin zamantakewar al'umma da suka kafa hukumomin ba da hidima ga kiwon lafiya a unguwoyin birane, irin wadannan asibitoci na mutane masu zaman kansu da aka kafa a unguwoyin birane za su iya samun karin kudin taimako daga wajen gwamnati tamkar yadda hukumomin gwamnati suke yi.

Ya bayyana cewa, gwamnati za ta kara karfinta wajen kula da harkokin samar da magungunan sha da ayyukan ba da hidimar kiwon lafiya a cibiyoyin ba da hidimar kiwon lafiya na unguwoyin birane da kuma rage farashin magungunan sha. Mr Jiang ya bayyana cewa, dukan mazauna za su iya biyan kudaden sayen magungunan sha , dukan farashin magungunan sha rahusa ne in an kwatanta su da na manyan asibitoci. (Halima)