Jam'iyyar Zhigong ta kasar Sin wata jam'iyyar siyasa ce wadda take hade da manyan mutanen Sinawa mazauna kasashen waje da suka dawo gida da 'yan iyalansu, wadda kuma take da halin musamman na kawancen siyasa, kuma ta dukufa kan aikin raya zaman gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, ita kuma wata jam'iyyar siyasa ce da ta shiga cikin harkokin kasa ta hanyar hadin gwiwa a tsakaninta da J.K.K.
An kafa Jam'iyyar Zhigong ta kasar Sin a watan Oktoba na shekarar 1925 a birnin San Francisco na kasar Amurka. Tun dogon lokacin da ya wuce, Jam'iyyar ta yi gwagwarmaya domin wadatar da kasa da kiyaye halaltaccen ikon Sinawa mazauna kasashen waje. A shekarar 1947 a Hongkong, Jam'iyyar ta kira taron wakilanta na 3 na duk kasar, kuma ta kama hanyar yarda da shugabancin J.K.S. da yin sabon juyin-juya halin demokuradiyya. A shekarar 1949, jam'iyyar ta aike da wakilanta don halartar taro na farko na dukkan wakilan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta farko ta jama'ar Sin, kuma ta shiga aikin zaben gwamnatin jama'a ta tsakiya.
Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949 kuma bisa halin da ake ciki a lokacin, Jam'iyya Zhigong ta kasar Sin ta juya hankalinta musamman kan ayyukan da take yi cikin kasar, kuma ta yi kokarin daukar mambobinta daga cikin manyan mutanen da suke da ikon wakiltar Sinawa mazauna kasashen wajen da suka dawo kasar da kuma 'yan iyalansu. Kuma ta kirayi dukkan mambobinta da su yi kokarin shiga ayyukan juyin-juya hali da gine-ginen zaman gurguzu, da ba da taimako ga sassan kula da harkokin Sinawa mazauna kasashen waje don sa kaimi ga tafiyar da ayyukan hadin gwiwa tsakanin Sinawa mazauna kasashen waje da kishin kasa da kyau.
Bayan da aka shiga cikin sabon lokacin tarihi, bisa matsayinta na wata jam'iyyar shiga harkokin kasa, Jam'iyyar Zhigong ta kasar Sin ta ba da babban taimako ga yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da bunkasa tattalin arzikin kasar. Kuma ta yi ayyuka da yawa a fannin karbar Sinawa mazauna kasashen waje da baki 'yan asalin kasar Sin wadanda suka dawo nan kasar Sin don yin yawon shakatawa da yin darussa da kuma zuba jari a kasar. Sa'an nan kuma ta kafa kungiyoyin wakilanta don kai ziyara a kasashen Amurka da Canada da sauran kasashe har sau da yawa domin sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashe waje. (Umaru)
|