Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-09 21:23:10    
Kungiyar Hezbollah ta Lebanon da Isra'ila suna ci gaba da musayar wuta

cri
Ran 9 ga wata, kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon da kasar Isra'ila suna ci gaba da musayar wuta a tsakaninsu. A ran nan da sassafe, sojojin kasar Isra'ila sun kai hare-hare ga sansanin 'yan gudun hijira na Ain Al Hilweh, wanda sansanin 'yan gudun hijira ne mafi girma na Palasdinawa a kasar Lebanon, inda mutane a kalla 2 suka rasa rayukansu, yayin da wasu 3 suka ji rauni. Daga baya kuma, dakarun Hezbollah sun mayar da martani a kudancin kasar Lebanon, inda sojojin kasar Isra'ila a kalla 10 suka mutu ko kuma suka jikata, yayin da suka rushe tankunan sojan kasar Isra'ila 4.

Ban da wannan kuma, a wannan rana, shugaban kasar Faransa Mr. Jacques Chirac ya bayyana cewa, bangaren kasar Faransa ya nemi a tanadi bukatar bangaren kasar Lebanon a cikin shirin kuduri na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wadda kasashen Faransa da Amurka suka tsara kan rikicin da ke tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila, yana kuma tsayawa tsayin daka kan ganin cewa, kasashen Lebanon da Isra'ila za su tsagaita bude wuta nan da nan.(Tasallah)